Nasara: 'Yan bindiga Sun Gane Kurensu Yayin da Jami'an Tsaro Suka Buɗe Musu Wuta a Arewa

Nasara: 'Yan bindiga Sun Gane Kurensu Yayin da Jami'an Tsaro Suka Buɗe Musu Wuta a Arewa

  • Yan bindiga sun ga takansu yayin da dakarun yan sanda suka far musu a yankin ƙaramar hukumar Kankara ta jihar Katsina
  • Mai magana da yawun yan sandan jihar, ASP Abubakar Aliyu, ya ce dakarun sun samu gagarumar nasara yayin wannan samame
  • A cewarsa, sun tarwatsa mafakar yan bindiga a kauyen Yargoje tare da kwato wasu muggan makamai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Dakaraun ƴan sanda sun kai samame maɓoyar ƴan ta'adda kuma sun daƙile mummunan nufinsu a kauyen Yargoje, ƙaramar hukumar Kankara a jihar Katsina.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta yanke hukuncin ƙarshe kan nasarar gwamnan PDP a zaben 2023

Sufetan yan sanda na kasa, IGP Kayode.
Yan Sanda Sun kai Samame Sansanin Yan Bindiga a Katsina, Sun Kwato Makamai Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

Ya ce dakarun ƴan sandan sun yi nasarar kwato bindigu guda huɗu tare da AK47 Magazine guda biyar a samamen da suka kai mafakar ƴan bindigan, cewar rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwan da kakakin 'yan sanda ya fitar ta ce:

"Jami'an yan sanda na caji ofis ɗin Kankara sun fita Operation ranar 21 ga watan Disamba, 2023 a yankin garin Yargoje, ƙaramar hukumar Ƙanƙara a jihar Katsina."
"Yayin haka suka yi wa maɓoyar miyagu dirar mikiya a kauyen Yar Gamji, wanda ya yi sanadin samun nasarar murƙushe ayyukan wata tawagar masu aikata ɗanyen aiki."
“Samamen da jam'ai suka kai shi cikin tsanaki da azama, ya haifar da kazamin artabu tsakanin jami’an rundunar ƴan sanda da gungun ‘yan bindigar."

Nasarar da yan sandan suka samu

Kakakin rundunar ƴan sanda, ASP Aliyu, ya ƙara da cewa sakamakon wannan artabu, yan sanda sun yi nasarar kwato manyan makamai daga hannun yan bindigan.

Kara karanta wannan

Labari mai daɗi: Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan ƙarancin takardun Naira, ta nemi afuwa

"Sakamakon haka ne ƴan sanda suka yi nasarar kwato bindigogin AK-47 guda biyu (2), bindigogin gida guda biyu (2), da kuma AK-47 Magazines guda biyar."

A cewarsa, wannan farmaki ya jefa yan ta'adda cikin mawuyacin hali a yanzu kuma dakaru na kan bin diddigi domin kamo waɗanda suka tsere.

Ƴan sanda sun dakile yunƙurin gona gidan gwamnatin Kano

A wani rahoton na daban Rundunar yan sandan Najeriya ta tabbatar da cewa wasu mutane sun yi ƙoƙarin babbake gidan gwamnatin jihar Kano.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Gumel ne ya bayyana haka yayin da ake dakon hukuncin kotun ƙoli kan zaben Gwamna Abba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262