Boye N600bn da Abubuwa 20 da Binciken Tinubu Ya Tono a ‘Badakalar’ Emefiele a CBN
- Binciken da Jim Obaze ya yi game da abubuwan da su ka faru a bankin CBN ya tona yadda aka saba doka
- Ana zargin lokacin Godwin Emefiele, an hada-kai da mataimakan gwamnonin CBN, an saci makudan kudi
- Kwamitin Obaze ya fallasa abubuwan da su ka kunshi badakalar da aka tafka da sunan tsarin e-Naira a CBN
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abuja - Premium Times ta tattaro zargin da ke wuyan Godwin Emefiele wanda ya jagoranci babban banki daga 2014 zuwa 2023.
Idan zargin sun tabbata, rahotanni sun nuna za a shigar da karar tsohon gwamnan bankin na CBN da wasu da su ka yi aiki a gwamnati.
An gano gwamnnan ya yi amfani da wasu mutane wajen sayaen bankuna a kasar.
StatiSense a shafinta na X da aka fi sani da Twitter, ta jero laifuffukan da kwamitin Obaze yake zargin an tafka a lokacin Mista Emefiele.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin da ake yi wa Godwin Emefiele a CBN
1. Ajiye kudi ba tare da izini ba a wasu asusun bankuna 593 da ke kasashen Birtaniya, Amurka da Sin.
2. Zare tsabar kudi fam miliyan $6.23 daga asusun CBN da sunan amincewar shugaban kasa domin biyan ‘yan kasar waje masu lura da zabe.
3. Manyan laifuffukan saba dokokin kudi da tsohon gwamnan bankin na CBN da wasu mutane 13 daga ciki har da mataimakan gwamnoni su ka aikata.
4. Dala miliyan £543.4m da Emefiele ya boye a asusu mai ribanya.
5. Badakalar juya farashin Naira a kasuwar canji.
6. Tafka sata a karkashin tsarin e-Naira da bankin CBN ya kawo.
7. Kawo canjin Naira ba tare da shawarar majalisar da ke kula da bankin CBN a lokacin ba.
8. Amincewa da canjin Naira ba tare da samun amincewar shugaban kasa a lokacin ba.
9. Bankin CBN ya buga N200, N500, N1,000 a kan N61.5bn.
10. Daga cikin kudin kwangilar canza kudi, CBN ya biya ‘dan kwangila N31.8bn.
11. An kashe N1.73bn da sunan wasu kudin shari’o’i 19 wanda aka gano alakar kudin da aikin canjin takardun Nairori.
12. Biyan £205,000 ga wani kamfanin Birtaniya a yunkurin buga takardun Nairori – samar da tambari, tsarin lambobi, da sauran matakan tsaro.
13. Cuwa-cuwar ba gwamnati bashin har N26.627tr.
14. Cuwa-cuwar wasu tsare-tsaren tallafi.
15. Cuwa-cuwar kashe kudi a lokacin COVID-19
16. Canza amincewar shugaban kasa wajen tsarin kamfanin NESI.
17. Cushen N198.96bn bayan samun amincewar shugaban kasa – aka maida N801.04bn ya zama Ntr.
18. Babu amincewar tsohon shugaban kasa, amma aka cire N500bn wajen ba gwamnati aron kudi.
19. Tsohon gwamnan da CBN da mataimakansa 4 sun hada-kai sun yi sata domin daidaita lissafin kudin babban banki.
20. Babu amincewa wajen bashin N22.7tr da aka gabatarwa majalisar tarayya domin samun damar ba gwamnati aron kudi ba tare da bin doka ba.
Binciken zargin badakalar Emefiele a CBN
Ana da labari Godwin Emefiele ya je kasashen Amurka, Ingila da Sin ya dankare biliyoyi ba tare da amincewar shugabannin CBN ba.
Binciken da Bola Tinubu ya sa ayi ya jefa tsohon gwamnan CBN da manyan Darektoci da na kusa da tsohon shugaban kasa a bala’i.
Asali: Legit.ng