Yar Najeriya Ta Koka Bayan Ta Bude Jakar Yar Aiki a Gida, Ta Ga Abubuwan Ban Mamaki a Ciki

Yar Najeriya Ta Koka Bayan Ta Bude Jakar Yar Aiki a Gida, Ta Ga Abubuwan Ban Mamaki a Ciki

  • Wata mata yar Najeriya ta ba da wani labari mai ban mamaki da ya wakana kwanan nan tsakanin iyalinta da yar aikinta
  • Kamar yadda ta bayyana, ta lura cewa mai aikinsu ta boye wasu kayayyakinta a cikin buhun shinkafa da nufin tserewa da su
  • Wannan abu da ta gano ya sa matar tana jin an ci mata amana sannan ta nemi sanin kudirin wadanda ta taimakawa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata matar aure ta caccaki mai aikinta kan kwashe mata kaya ba tare da saninta ba.

Matar mai suna @brownmelarnie a dandalin X ta ce yar'uwarta ta samu kira daga mai aikinta, tana mai sanar da ita game da wani kunshi da take so a kai mata kauye.

Kara karanta wannan

Ina za ki damu: Mata ta hada baki da mijinta sun hallaka abokinsa a Kano

Mata ta gano mai aiki na kwashe mata kaya
An yi amfani da hoton don misali ne kawai, ba su da alaka da labarin Hoto: Bettmann/ NurPhoto/ Getty Images.
Asali: Getty Images

Mata ta ba da labarin yadda mai aiki sace mata kaya da kokarin tserewa da shi

Sai dai kuma, kiran da aka yi mata ya darsa shakku a zuciyarta. An ce kunshin na dauke da buhun shinkafa, amma yanayin tattaunawar ya sanya su farkawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar da iyalinta sun shiga yanayin son sanin halin da ake ciki yayin da suka yanke shawarar bincika buhun shinkafar. Ga mamakinsu, maimakon ganin kayan hatsin da ake magana a kai, sai su gano cewa kayan amfaninsu ne a ciki.

Tufafi mallakin matar da diyarta, gashi yan kanti, kayan kwalliya daga jakar aikinta, harma da sakin mahaifiyarta a cikin kayan da aka nade a ciki.

Mata ta bankado shirin mai aikinta, ta fallasa ta

Don ganin ta kamo bakin zaren amanar da aka ci mata, matar da iyalinsa sun tambayi mai gadi, wanda ya bayyana cewa mai aikin ce ta sako da kayan kasa.

Kara karanta wannan

Kyakkyawar budurwa ta fashe da kuka bayan samun kyautar N20k don ta biya kudin makaranta

Da farko, mai aikin ta yi kokarin cin musu, amma da aka yanke shawarar duba kamarar CCTV, sai ta fadi gaskiya.

Jama'a sun yi martani

@tuyonspeaks ta yi martani:

"Wato, ta so ku taya ta isar da sakon kayayyakin da ta sace maku?"

@MichelleAJobes ta ce:

“Haaaaa.”

@CliffPresta ta yi martani:

“Ahhhh.”

Ga wallafar tata a kasa:

Direba ya tsinci jakar kudi a motarsa

A wani labari na daban, mun ji cewa wani direban tasi da ba a bayyana sunansa ba ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ya mayar da bandir-bandir na kudi da wani fasinja ya manta a motarsa.

Portharcourt Specials, wanda ya kawo rahoton ya saki wani bidiyo da ke nuna yadda mutanen biyu suka bude bakar jakar sannan suka fitar da bandir-bandir na kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng