Matattu Ma Basu Tsira Ba Yayin da 'Yan Fashi Suka Yi Wa Gawa Tatas a Cikin Mota, Bayanai Sun Fito

Matattu Ma Basu Tsira Ba Yayin da 'Yan Fashi Suka Yi Wa Gawa Tatas a Cikin Mota, Bayanai Sun Fito

  • 'Yan fashi sun yi wa wani mataccen mutum sata karkaf a cikin motarsa a birnin Benin City da ke jihar Edo
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a birnin Benin City da ke jihar a ranar Laraba 20 ga watan Disamba
  • Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Chidi Nwabuzor ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Alhamis 21 ga watan Disamba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Wasu tsagera da ake zargin 'yan fashi ne sun yi wa gawar wani mutum sata a cikin motarsa da ke jihar Edo.

Lamarin ya faru ne a birnin Benin City da ke jihar a ranar Laraba 20 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya rabawa ma'aikata N100,000 don bikin kirsimeti

'Yan fashi sun lalume wata fawa a cikin mota a Edo
Ana zargin 'yan fashin sun kwashe wa mamacin kayayyakinsa. Hoto: NPF.
Asali: Facebook

Mene ake zargin 'yan fashin da aikata wa?

Daily Trust ta tattaro cewa ba a samu labarin faruwar lamarin ba sai da safiyar jiya Alhamis 21 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit ta tattaro cewa rundunar 'yan sanda ne ta gano mutumin kan siterin motar an bincike dukkan aljifayensa da kuma dauke wayarsa.

Rundunar bangaren binciken laifuka a jihar ta bayyana cewa ta na neman hanyar da zata bi don sanin iyalan mamacin.

Yayin da aka tuntube shi, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Chidi Nwabuzor ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Alhamis 21 ga watan Disamba.

Chidi ya ce abin da rundunarsu ta samu kawai shi ne rasiti mai dauke da sunan Dakta Eromon David.

Wane martani 'yan sanda suka yi?

Ya ce an samu gawar mamacin a cikin wata mota kirar Toyota a kwanar Ikpokpan da ke kusa da GRA a birnin Benin City.

Kara karanta wannan

Bikin Kirsimeti: Yan sanda sun gano bindigu an boye su cikin buhu a wata jihar Kudu

Ya ce:

"Yan fashin sun yi wa mamacin tatas yadda hatta aljifayen wandonsa an fito dasu wanda ke nuna sun kwashe komai.
"An samu rasiti guda uku na Jami'ar Benin da muka duba sunan sai muka ga ya na dauke da Dakta Eromon David."

A tsare matashi kan burme abokinsa a Kano

A wani labarin, Babbar kotun jihar Kano ta gurfanar da wani matashi kan zargin burme abokinsa da wuka a ciki.

Wanda ake zargin, Musbahu Yau ya caka wa abokin nasa ne saboda wata 'yar hatsaniya da ta faru a tsakaninsu..

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.