Mutane 3 Sun Tsere Daga Sansanin ’Yan Bindiga Bayan Sun Yi Tatil a Kaduna, Bayanai Sun Fito
- Yayin da mahara su ka yi tatil da giya su na bacci, wasu daga cikin wadanda suka kama sun tsere da tsakar dare
- Mutanen uku daga cikin 11 da aka yi garkuwa da su sun tsere ne a daren ranar Juma’a a kauyen Azzara da ke jihar Kaduna
- Maharan sun farmaki Unguwar Tudu a kauyen inda suka hallaka soja da kuma garkuwa da mutanen guda 11 tare da mai gida da iyalinsa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna – Wasu daga cikin mutane 11 da aka sace a kauyen Azzara a karamar hukumar Kachia sun tsere daga hannun mahara.
Daily Trust ta ruwaito cewa ‘yan bindiga sun sace mutanen a ranar 6 ga watan Disamba a jihar Kaduna.
Yaushe maharan suka kai harin?
Maharan sun mamaye Unguwar Tudu a kauyen inda suka hallaka soja da kuma garkuwa da mutanen guda 22 tare da mai gida da iyalinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Danjuma Saleh, wani mazaunin kauyen Azzara ya ce mutanen uku sun tsere ne a ranar Litinin da dare bayan maharani sun bugu da giya sun yi bacci.
Ya ce:
“A safiyar yau (Talata) ce da misalin karfe 5 na safe Dagacin kauyen Akilbu ya kira Dagacin Azzara inda ya ce wadanda suka tseren su na tare da shi.”
Wane martani 'yan sanda suka yi?
Danjuma ya ce ‘yan uwan wadanda aka sacen sun yi magana dasu yayin da aka dauke su zuwa asibiti don duba lafiyarsu.
Babu wata sanarwa a hukumance daga kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar kan tserewar wadannan bayin Allah har zuwa lokacin tattara wannan rahoto.
Arewa maso Yamma na fama da hare-haren 'yan bindiga musamman a yankunan karkara.
An tsare matashi kan zargin burme abokinsa
A wani labarin, An gurfanar da wani matashi kan zargin burma wa abokinsa wuka a ciki kan wata ‘yar hatsaniya a tsakaninsu.
Wanda ake zargin, Musbahu Yau ya caka wa abokin nasa wuka a ciki har sai da hanji ya fito waje.
Lamarin ya faru ne a jihar Kano yayin da ake tsaka da sauraran shari’ar zaben gwamnan jihar a jiya Alhamis.
Asali: Legit.ng