Labari Mai Daɗi: Gwamnatin Tinubu Ta Yi Magana Kan Ƙarancin Takardun Naira, Ta Nemi Afuwa

Labari Mai Daɗi: Gwamnatin Tinubu Ta Yi Magana Kan Ƙarancin Takardun Naira, Ta Nemi Afuwa

  • Gwamnatin tarayya ta baiwa ƴan Najeriya haƙuri kan karancin takardun kuɗin da ya dawo sabo a ƴan kwanakin nan
  • Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Muhammed Idris, ya ce matsalar da aka shiga ba da gangan aka kawo ta don kuntata wa mutane ba
  • Ya ce babban bankin Najeriya na aiki tukuru domin shawo kan lamarin daga nan zuwa sabuwar shekara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Gwamnatin tarayyan Najeriya karkashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta roƙi afuwar ƴan Najeriya kan dawowar matsalar ƙarancin takardun Naira.

Da take rarrashin ƴan Najeriya ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba, 2023, FG ta bayyana cewa ƙarancin kuɗin zai ƙare a sabuwar shekara mai kamawa 2024.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta amince da buƙatar Tinubu a kotun koli ana shirin yanke hukunci kan zaben Kano

Karancin naira.
Karancin Takardun Kuɗi Zai Wuce a Sabuwar Shekara In Ji Ministan Tinubu Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a na kasa, Mohammed Idris, ya ce karancin takardun kuɗin da ake fuskanta ba da gangan bane, kamar yadda The Nation ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idris ya yi wannan bayanin ne yayin da yake jawabi kan nasarorin da gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Tinubu ta samu kawo yanzu da kalubalen da take fuskanta.

Yaushe FG zata kawo karshen karancin kuɗi?

Ministan yaɗa labaran ya kuma tabbatar wa ƴan Najeriya cewa nan da sabuwar shekara za a samu ƙarin takardun kuɗi a hannun jama'a.

Ya ce babban bankin Najeriya (CBN) na yin duk mai yiwuwa domin ganin ya kawar da ƙarancin kuɗin nan da ɗan ƙankanin lokaci.

Muhammad Idris ya ce:

"Game da karancin Naira, gwamnatinmu tana sane da cewa akwai wannan koken na ‘yan Najeriya kan karancin kudin Naira kuma tuni CBN ya fara aiki a wannan bangaren."

Kara karanta wannan

Kotun koli na shirin yanke hukunci, wasu tsageru sun yi yunƙurin ƙona gidan gwamnatin Kano

"Za a kara buga sabbin takardu da sauransu a sake su kuma ‘yan Najeriya za su samu karin takardun Naira da za su kashe. Ba da gangan aka kawo wannan wahalar don kuntatawa mutane ba."
"Ba haka abun yake ba, mai yiwuwa matakan da babban banki CBN ke ɗauka ne ya jawo naƙasu na wucin gadi amma komai zai wuce."

Martanin wasu yan Najeriya

Wasu ƴan Najeriya a jihar Katsina sun shaida wa Legit Hausa cewa sun yi tsammanin wannan matsalar karancin Naira ta wuce har abada tunda aka tsige Emefiele.

Umar Ibarhim ya bayyana mana cewa ya yi mamaki loƙacin da ya je cire kuɗi wurin masu POS aka ce masa babu, yana mai cewa ya kamata a magance matsalar.

A kalamansa:

"Ni ban san meke faruwa ba sai da kuɗin aljihuna suka kare, na je wurin KB (Mai POS a garin Dabai) ya ce mun ba bu sai dai na jira, na wuce wurin wani shi ma babu."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun ƙara kai mummunan hari kan masu shirin bikin addini a jihar arewa

"Sai da naje wurin Abubakar sannan na samu, shi ma ya ce da kyar suke samu shiyasa suka ƙara kudin cajin da suke karɓa."

Abdulbashi Salisu, mai sana'ar POS ya ce ya rabu da zuwa banki neman tsabar kuɗi domin ba su ba shi adadin da yake buƙata.

Shugaba Bola Tinubu Ya Dira Jihar Legas

A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu ya isa jihar Legas tare da hadimansa domin yin hutun bikin kirsimeti mai zuwa a mako na gaba.

Gwamna Babajide Sanwo-olu da mataimakin gwamnan Legas, Obafemi Hamzat, ne suka tarbi mai girma shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel