"Kebbi N690/Lita": An Kara Farashin Man Fetur Daf Da Kirsimeti, Jihohi 3 Za Su Fi Siya Da Tsada
- Najeriya ta sake samun ƙarin farashin man fetur a faɗin ƙasar nan a watan Nuwamba na shekarar 2023
- Farashin da nuna a rahoton farashin NBS na baya-bayan nan ya nuna ƙaruwar sama da kaso 200% duk shekara
- A cikin jihohin Najeriya da suka fi tsadar farashi, jihohin Arewa ne a kan gaba, waɗanda suka hada da Kebbi, Jigawa, da Adamawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa matsakaicin farashin Man PMS wanda aka fi sani da man fetur ya ƙaru zuwa Naira 648.93 kan kowace lita a watan Nuwamba 2023.
Wannan yana nuna ƙaruwar kaso 220.49% idan aka kwatanta da matsakaicin farashin N202.48 da aka biya a watan Nuwamban 2022.
NBS ta bayyana hakan ne a sabon rahotonta na duba farashin man fetur da ta fitar a ranar Alhamis, 21 ga Disamba, 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda farashin man fetur yake a Najeriya
Rahoton ya kuma nuna cewa a canjin wata-wata, matsakaicin farashin dillalan ya ƙaru da kashi 2.90% daga N630.63 a watan Oktoban 2023.
Sauye-sauyen da aka samu sun nuna yadda aka cire tallafin man fetur da ƴan Najeriya ke morewa tsawon shekaru.
Jihohin Najeriya da suka fi tsada da ƙarancin farashin man fetur
A nazarin jiha-jiha kan farashin man fetur, bayanan NBS sun nuna cewa mutanen jihar Kebbi sun biya kuɗin man fetur na dillalai mafi tsada na N691.00 kan kowace lita.
Sai kuma jihohin Jigawa da Akwa Ibom da farashin man fetur N677.67 da kuma N675.00 kan kowace lita a watan Nuwamban 2023.
Saɓanin haka, jihohin Taraba, Kaduna da Legas sun kasance masu mafi ƙarancin farashin dillalan man fetur a kan N618.00, N620.29 da N623.12, bi da bi.
A bangaren shiyya kuwa, shiyyar Kudu-maso-Kudu ta kasance mafi girman farashin dillali na N663.59, yayin da shiyyar Arewa maso Gabas ke da mafi ƙarancin farashin N632.75.
Mazauna Arewa maso Yamma, Arewa ta Tsakiya, Kudu maso Yamma, da kuma Kudu maso Gabas sun biya N659.17, N647.43, N636.47 da N653.07, bi da bi.
Akwai Yiwuwar Saukar Farashin Mai
A wani labarin kuma, kun ji cewa akwai yiwuwar farashin man fetur da ya yi tashin gwauron zaɓi a ƙasar nan ya sauka.
Kamfanin NNPCL ya bayyana cewa hakan zai yiwu ne saboda damar da ya ba ƴan kasuwa su shigo da man cikin ƙasar nan.
Asali: Legit.ng