Majalisar Dokokin Jihar Sokoto Ta Kamo Hanyar Magance Rashin Tsaro a Jihar Bayan Ta Yi Wani Abu 1
- Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya gabatar da ƙudiri a gaban majalisar dokokin jihar domin kafa rundunar tsaro ta 'Community Guards Corps'
- Majalisar ta amince da ƙudirin bayan ta kafa kwamitocin haɗin gwiwa waɗanda suka yi nazari kan ƙudirin tare da bayar da rahotonsu
- Amincewa da ƙudirin na nufin gwamnatin jihar ta samu sahalewar majalisar domin kafa rundunar wacce za ta taimaka wajen samar da tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Majalisar dokokin jihar Sokoto ta amince da ƙudirin da Gwamna Ahmed Aliyu ya gabatar a gabanta domin kafa rundunar tsaro a jihar.
Majalisar dokokin a ranar Laraba, 20 ga watan Disamba ta amince da a kafa rundunar tsaro ta 'Community Guards Corps' a jihar, cewar rahoton The Punch.
Amincewa da ƙudirin ya biyo bayan nazarin rahoton da kwamitocin haɗin gwiwa kan ayyuka na musamman da harkokin tsaro, ɓangaren shari’a da kare hakkin bil’adama suka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa majalisar ta amince da ƙudirin?
Shugaban kwamitin, Alhaji Nasiru Adamu (PDP-Goronyo), ya bayyana cewa an yi nazari sosai kan ƙudirin dokar, wanda ya haifar da shawarwari 28, rahoton New Telegraph ya tabbatar.
Waɗannan shawarwarin sun hada da canza sunan kudirin zuwa:
"‘Kudirin dokar kafa rundunar tsaro ta Community Guards Corps ta jihar Sokoto' da samar da tsaro da zaman lafiya da tsaron lafiyar mutane da dukiyoyinsu, da kuma gaggauta kai agajin gaggawa." A cewarsa.
Adamu ya ƙara da cewa akwai buƙatar a samar da wani sabon sashe dangane da adadin jami’an da za su yi aiki da kuma gyara kura-kuran rubutu daga sashen da ke kula da harkokin shari’a.
Shugaban majalisar Alhaji Tukur Bala ya gabatar da rahoton domin dubawa, kuma ƴan majalisar sun amince da shi ta hanyar kaɗa ƙuri’a.
Gwamnan Katsina Ya Kaddamar da Rundunar Tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umaru Radda, ya ƙaddamar da rundunar 'Community Watch Corps' domin samar da tsaro a jihar.
Yayin da yake kaddamar da rukunin farko na rundunar, Radda ya ce hakan na cikin kokarin gwamnatinsa na daukar wani tsari na "al'umma" don magance rashin tsaro da ya addabi jihar.
Asali: Legit.ng