An Cafke Matasa 5 Kan Mallakar Bindigu a Kauyen Katsina, Yadda Su Ka Samu Makamin Ya Ba da Mamaki

An Cafke Matasa 5 Kan Mallakar Bindigu a Kauyen Katsina, Yadda Su Ka Samu Makamin Ya Ba da Mamaki

  • Rundunar ‘yan sanda ta yi nasarar kama wasu matasa biyar da zargin mallakar makami a jihar Katsina
  • Ana zargin matasan ne da mallakar bindiga kirar AK-47 a kauyen Kurmi da ke karamar hukumar Bakori
  • Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Abubakar Sadiq Aliyu shi ya tabbatar da haka a jiya Laraba 20 ga watan Disamba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina – Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta cafke wasu mutum biyar da mallakar bindigu.

An kama matsana ne da bindiga kirar AK-47 a kauyen Kurmi da ke karamar Bakori da ke jihar, cewar Punch.

'Yan sanda sun cafke matasa 5 kan zargin mallakar bindigu
An kama matasan ne a kauyen Kurmi da ke jihar Katsina. Hoto: Dikko Radda.
Asali: Facebook

Mene rundunar 'yan sanda ta ce?

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Abubakar Sadiq Aliyu shi ya tabbatar da haka a jiya Laraba 20 ga watan Disamba ga manema labarai.

Kara karanta wannan

Harin sojojin Najeriya kan farar hula: Miyetti Allah ta kafa wa Tinubu wani muhimmin sharadi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sadiq ya ce sun samu nasarar cafke matasan ne bayan samun bayanan sirri daga jama’a da kuma ‘yan sa kai, cewar Newstral.

Ya ce:

“A ranar 19 ga watan Disamba, mun samu bayana sirri daga jami’anmu da ke ofishinmu a Bakori da hadin gwiwar ‘yan sa kai.
“Wannan hadin gwiwa ita ta yi sanadin kama wadanda ake zargin su guda biyar a kauyen Kurmi.
“Daga cikin wadanda ake akwai Sharhabilu Dahiru mai shekaru 20 sai Abubakar Tukur dan shekara 25 da Sulaiman Sanusi mai shekaru 20.
"Sauran sun hada da Kasamanu Abdullahi mai shekaru 20 sai kuma Abdulrahman Shu’aibu mai shekaru 20 shi ma.”

Wane martani wadanda ake zargin su ka yi?

Kakakin rundunar ya ce dukkan wadanda ake zargin sun fito ne kauyen Kakumi da ke karamar hukumar Bakori a jihar Katsina, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, yan majalisar dokoki sun ɗauki sabon mataki ƙan yunkurin tsige gwamnan PDP

Ya ce wadanda ake zargin sun tabbatar da tuhumar da ake a kansu inda su ka ce sun sace makamin ne a wurin wani mai suna Jamilu Lawal.

Sadiq ya kara da cewa saboda girman laifin mallakar bindiga an gayyaci Jamilu don amsa tambayoyi kan zargin mallakar makami.

Sojoji sun hallaka kasurgumin dan bindiga

A wani labarin, rundunar soji ta yi nasarar hallaka wani kasurgumin dan bindiga a jihar Kebbi.

Marigayin mai suna Mainasara ya rasa ransa ne bayan wani farmaki da rundunar ta kai a jihar ‘yar bazata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.