Jerin Gwamnonin Najeriya 3 Da Suka Rattaba Hannu Kan Kasafin Kudin 2024 a Jiharsu

Jerin Gwamnonin Najeriya 3 Da Suka Rattaba Hannu Kan Kasafin Kudin 2024 a Jiharsu

  • Shekarar 2023 na shirin karewa, gwamnonin jihohin Najeriya sun gabatar da kasafin kudin 2024 ga majalisar jiharsu don amincewa
  • A yayin da wasu gwamnonin ke jiran rahoto daga majalisar jihohinsu, tuni gwamnoni uku suka rattaba hannu kan kasafin kudinsu har ya zama doka
  • Wannan na nuna irin hadin kai da ke tsakanin gwamnoni da 'yan majalisun jiharsu, kamar yadda aka gani a jihohjin Katsina, Plateau da Delta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Akalla gwamnoni uku ne suka rattaba hannu kan kasafin kudin 2024 na jiharsu, wanda ke nuni da cewa yanzu kasafin ya zama doka, abin da ya rage kawai a aiwatar da shi a aikace.

Ba kowacce jiha ce take samun saurin amincewar kasafinta daga majalisar jihar ba, wasu lokutan kuma akan samu tsaikon ne daga su kansu gwamnonin.

Kara karanta wannan

Kotu ta garkame matasa 2 kan kashe abokinsu saboda shinkafa

Gwamnoni uku sun rattaba hannu kan kasafin 2024 na jiharsu
Gwamnonin Katsina, Plateau da Delta sun rattaba hannu kan kasafin kudin jiharsu. Hoto: @dikko_radda, @RtHonSheriff, @CalebMutfwang
Asali: Twitter

Ga jerin gwamnonin da suka sa hannu kan kasafin 2024 na jiharsu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jihar Katsina

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya sa rattaba hannu kan kasafin 2024 bayan da majalisar jihar ta amince da shi, hakan na nufin kasafin ya zama doka.

A ranar Laraba gwamnan ya sa hannu kan kasafin da ya kai kiyascin naira biliyan 454.308, kuma ya gode wa majalisar jihar da ta amince da kasafin cikin sauri.

Jihar Plateau

A jihar Plateau kuwa, Gwamna Caleb Mutfwang ya saka hannu kan kasafin kudin jihar da ya kai naira biliyan 314.8, kamar yadda daraktan wata labaran jihar Gyang Bere ya sanar.

Kasafin 2024 na jihar mai taken 'Kasafin sabuwar rayuwa', ya kunshi naira biliyan 152.5 don manyan ayyuka da kuma naira biliyan 162.3 na ayyukan yau da kullum.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya rabawa ma'aikata N100,000 don bikin kirsimeti

Jihar Delta

Haka take a jihar Delta, inda shi ma Gwamna Sheriff Oborevwori a ranar Laraba ya sa hannu kan kasafin 2024 na jihar da ya kai naira biliyan 724.979, bayan majalisar jihar ta amince da shi.

Oborevwori ya ce kasafin zai tabbatar da cewa tattalin arzikin ya bunkasa, la'akari da an ware naira biliyan 316,624 don ayyukan yau da kullum da kuma naira biliyan 408,354 don manyan ayyuka.

Majalisar Kano ta amince da kasafin da Gwamna Yusuf ya gabatar mata

A wani labarin kuma, Legit ta ruwaito maku cewa majalisar jihar Kano ta amince da kasafin kudin 2024 da gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya gabatar mata.

Tun da fari Gwamna Yusuf ya gabatar da naira biliyan 350 matsayin kasafin, amma majalisar ta mayar da shi naira biliyan 437 don gudanar da wasu ayyukan jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.