Yan Sanda Sun Kama Mutum 2 da ke Yin Jabun Lemun Kwalba, Sun Saki Bidiyon Kamfanin da Sauransu
- Rundunar yan sanda a jihar Lagas ta bankado wani gini inda ake yin jabun lemukan kwalba
- A cewar kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin, an kama yan Najeriya biyu da ke kula da kamfanin
- Rundunar yan sandan ta saki bidiyoyin kamfanin wanda ke dauke da lemuka masu guba da aka yi, kuma za a siyarwa yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Lagos - Rundunar yan sandan jihar Lagas, reshen Ojo, sun kama wani Mista Imo Lawrence mai shekaru 35 da Mista Magnus Nwonka mai shekaru 42 a ranar Laraba, 20 ga watan Disamba, dauke da wasu jabun lemuka.
Rundunar ta sanar da hakan ne a cikin wata wallafa da kakakinta, Benjamin Hundeyin, ya yi a shafin X (wanda aka fi sani da twitter a baya), tare da hoto da bidiyon wadanda ake zargin.
Kamar yadda Hundeyin ya bayyana, a yayin gudanar da bincike, wadanda ake zargin sun jagoranci jami’an ‘yan sanda zuwa masana’antarsu mai dauke da dakuna da yawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ana ci gaba da bincike," in ji Hundeyin.
NAFDAC ta dira a kamfanin magunguna
A wani labarin, mun ji cewa hukumar kula da abinci da magunguna ta NAFDAC ta kai samame kamfanin hada magungunan gargajiya na Baban Aisha da ke Kaduna.
Kamfanin hada magungunan gargajiyan da ke Tafa kan hanyar Kaduna zuwa Abuja an rufe shi ne sakamakon samun korafi daga wasu mutane a yankin.
Umar Sulaiman shugaban bangaren bincike na hukumar ya ce wannan rangadi suna yi ne don kiyaye lafiyar al'umma, cewar Daily Nigerian.
NAFDAC ta magantu kan Indomie
A gefe guda, hukumar Kula Da Ingancin Abinci Da Magunguna Ta Kasa (NAFDAC), ta bayyana sakamakon binciken da ta gudanar a kan taliyar Indomie.
Darakta janar ta hukumar, Farfesa Christianah Adeyeye ce ta bayyana haka ranar Alhamis a Legas, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Hukumar ta bincika indomin domin ganin ko ta na ɗauke da sinadarin Ethylene Oxide ko nau'o'insa, wanda sinadari ne mai matuƙar haɗari ga lafiyar ɗan Adam.
A binciken da aka gudanar, an gano cewa taliyar indomin wacce ake yi a Najeriya, da kuma kayan yajinta basa ɗauke da waɗannan sinadarai masu cutarwa.
Asali: Legit.ng