Yan Sanda Sun Ragargaji Yan Bindiga, Sun Ceto Mutanen da Suka Sace

Yan Sanda Sun Ragargaji Yan Bindiga, Sun Ceto Mutanen da Suka Sace

  • Rundunar ƴan sandan juhar Taraba ta samu gagarumar nasara kan miyagun ƴan bindigan da ke kai hare-haren ta'addanci a jihar
  • Jami'an rundunar sun samu nasarar halaka wasu ƴan bindiga mutum uku a wani samame da suka kai maɓoyarsu a ƙaramar hukumar Yoro
  • Ƴan sandan sun kuma samu nasarar ceto mutanen da ƴan bindigan suka sace a wani hari da suka kai ƙauyen Pupule

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Rundunar ƴan sandan jihar Taraba ta sanar da samun nasarar kashe ƴan bindiga uku tare da kuɓutar da wasu mutane da dama da aka yi garkuwa da su.

Sai dai, a yayin artabun da ƴan bindigan, wani mataimakin Sufeton ƴan sanda ya rasa ransa, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun sheke dan bindiga sun kwato muggan makamai a Kaduna

Yan sanda sun halaka yan bindiga a Taraba
Yan sanda sun halaka yan bindiga uku a Taraba Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

A cewar Usman Abdullahi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, ƴan sandan sun gudanar da aikin ceto mutum 23 da aka yi garkuwa da su ranar Talata a ƙauyen Pupule da ke ƙaramar hukumar Yoro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'in ɗan sanda ɗaya ya rasa ransa

Jaridar Daily Post ta ce musayar wutar da aka yi a lokacin da ake ƙoƙarin kuɓutar da mutanen ya yi sanadiyyar mutuwar jami'in ɗan sanda mai suna ASP Aminu Nuhu.

Abdullahi ya lura cewa an yi musayar wuta mai tsanani ne a wani yanki mai tsaunuka a ƙaramar hukumar Yoro, inda ake zargin maɓoyar ƴan bindigan ne.

Yayin da aka kashe ƴan bindiga uku, wasu da dama sun samu raunukan harbin bindiga tare da yin nasarar tserewa.

Bugu da ƙari, ƴan sanda sun kama wasu ƴan bindiga huɗu a yayin samamen.

Kara karanta wannan

Kungiyar kwadago ta kasa ta yi wa Shugaba Tinubu da CBN babbar barazana kan abu 1 tak

"Dakarun rundunar ƴan sandan da ke yaƙi da garkuwa da mutane ne ke gudanar da aikin ceton." A cewar kakakin.

Sojoji Sun Sheke Dan Bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar sojoji ta ɗaya da ke Kaduna ta samu nasarar halaka wani ɗan bindiga a yayin wani kwanton ɓauna da ta yi wa wasu miyagun ƴan bindiga.

Ayayin kwanton ɓaunan wanda sojojin suka yi wa ƴan bindigan a ƙauyen Sabon Birni cikin ƙaramar hukumar Igabi, sun samu nasarar ƙwato muggan makamai a hannun ƴan bindigan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng