"Kudin Ka Mutuncin Ka", Dino Melaye Ya Ba 'Yan Najeriya Shawarar Su Tashi Su Nemi Arziki

"Kudin Ka Mutuncin Ka", Dino Melaye Ya Ba 'Yan Najeriya Shawarar Su Tashi Su Nemi Arziki

  • Jigon PDP Dino Melaye ya garzaya soshiyal midiya don baje kolin sabuwar motar da ya siya sannan ya yi shagube ga yan Najeriya
  • Dan takarar gwamnan na Kogi a zaben 11 ga watan Nuwamba ya bukaci yan Najeriya da su yi aiki tukuru don gujin jawabi mara amfani a gaba
  • A cikin bidiyon da ya yadu, an caccaki Melaye kan shan kaye a zaben gwamnan Kogi watanni bayan ya fadi zaben sanata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a zaben ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, a jihar Kogi, Dino Melaye ya aika muhimmin sako ga yan Najeriya.

Yayin da yake baje kolin tsadaddiyar motarsa sabuwa fil, Melaye ya bukaci yan Najeriya da su ci gaba da yin aiki tukuru don kada su zo suna wakar da bata da amfani.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa yaki da shugabannin Najeriya bai da amfani, Malamin addini

Dino Melaye ya shawarci yan Najeriya da su nemi kudi
"Kudin ka mutuncin ka", Dino Melaye ya ba 'yan Najeriya shawarar su tashi su nemi arziki Hoto: @_dinomelaye
Asali: Twitter

Ya yi wannan hasashen ne a cikin wani bidiyo da ya yadu, wanda ya wallafa a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) a ranar Laraba, 20 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake bin sautin wata waka da ke tashi a cikin mota kirar Bentley, Dino ya yi wa bidiyon take da:

"Kada ka je ga nemi kudi faaaa. Daga baya ka zo kana karanto a banzan bazara. rayuwa daya ce."

Yan Najeriya sun yi martani ga bidiyon Dino

Kamar kullun, yan Najeriya sun garzaya sashin sharhi na shafin Dino sannan suka yi martani ga ci gaban. Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martaninsu a kasa:

@efewonyi ya rubuta:

"Ya nuna karara cewa mutumin nan ya yi amfani da zaben wajen tara kudi ne."

@FunnyliticaJoke ta rubutaL

Kara karanta wannan

Direban tasi ya tsinci jakar kudi a motarsa, bidiyo ya bayyana yayin da ya mayar da shi

"Shakka babu cewa Dino talaka ne da yake tasowa. Don haka yake amfani da damar tserewa da ya yi a yanzu da girma ya zo. Lol."

@tobbiematthew ya yi martni:

"Ya kamata mutanen Kogi su dunga zuwa addu'an godiya duk ranarar Lahadi na kowani wata."

@KennyNuga ya rubuta:

"Dino ya ci gaba da harkokin gabansa duk da kayen da ya sha a zaben gwamna a Kogi.
"Gwanda ya ji dadin sauran kudinsa maimakon ya koka kan dan madarar da ya gugguba, DINO, yaro mai hikima."

@iniestasolobaby ya rubuta:

"Lallai Yahaya bello ya lalata wannan mutumin. Ji yadda ya kaskantar da shi."

Dino ya karyata siyan kuri'u

A wani labarin, mun ji a baya cewa an zargi Dino Melaye, dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamna da aka yi a ranar 11 ga watan Nuwamba, a jihar Kogi, da siyan kuri'u.

A cikin wani rahoto a ranar Alhamis, 16 ga watan Nuwamba, Sahara Reporters ta yi zargin cewa Melaye, wanda ya zo na uku a zaben, ya fusata sannan ya nemi wasu mambobin jam'iyya a jihar da su dawo masa da kudinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel