Murna Yayin da Gwamnati Ta Amince da Kyauta Mai Gwabi Ga Ma'aikata Domin Kirsimeti
- Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya amince da Naira 100,000 a matsayin kyautar Kirsimeti ga ma’aikatan jihar da ke karɓar albashi
- Wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar, Warisenibo Johnson, ta bayyana hakan a yammacin ranar Talata, 19 ga watan Disamba
- Wannan gagarumin matakin da gwamnan ya ɗauka na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da takun saƙa tsakaninsa da magabacinsa, Nyesom Wike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Port Harcourt, jihar Rivers - Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa ya amince da Naira 100,000 a matsayin kyautar Kirsimeti ga ma’aikatan jihar.
Warisenibo Joe Johnson, kwamishinan yada labarai da sadarwa, ya ba da wannan bayanin kwanaki shida kafin zuwan Kirsimeti.
Gwamna Fubara ya ba da izinin a ranar Talata, 19 ga watan Disamba, domin aiwatarwa da gaggawa domin ba ma'aikatan gwamnati damar yin bikin Kirsimeti cikin walwala.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PM News ta ce Warisenibo ya tabbatar da wannan gagarumin halaccin gwamnan cikin wata sanarwa da ya aike musu.
Har ila yau, jaridar Leadership, ta tabbatar da bayar da wannan kyautar kuɗin ga ma'aikatan.
Kyautar Kirsimeti na Rivers: Ƴan soshiyal midiya sun yi martani
Biyo bayan wannan sanarwar, masu amfani da yanar gizo sun yi martani a kai. Ga kaɗan daga ciki a nan ƙasa:
@sograns ya rubuta:
"Bayan shekaru 16, yanzu ma'aikatan jihar Rivers sun samu kyautar Kirsimeti a ƙarƙashin Sir Siminalayi Fubara. Allah ya albarkaci Sim!"
@fareedarhTofa said:
"Shawarar da Fubara ya yanke na bayar da kyautar Kirsimeti ga ma’aikatan gwamnati abu ne mai karamci da tunani, zai kawo wa iyalai da yawa agajin kuɗi a lokacin hutu, kuma hakan ya nuna jajircewa wajen kyautata jindaɗin ma’aikatan jihar. Godiya ga Fubara bisa yin wannan aikin!"
Suleiman Qasim ya rubuta:
"Babbar garaɓasa."
Sanwo-Olu Ya Ƙara wa Ma'aikata Albashi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya amince da yin ƙarin albashin N35,000 ga ma'aikatan jihar.
Gwamnan ya kuma amince a biya kaso 50% na albashin watan Disamba a matsayin alawus na ƙarshen shekara ga dukkan ma'aikata da masu riƙe da muƙaman gwamnati.
Asali: Legit.ng