Babban Hafsan Tsaro Ya Aike da Sako Mai Muhimmanci Ga Yan Najeriya Kan Jefa Bam Ga Musulmi a Kaduna
- Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya (CDS) bai ji daɗin kalaman da wasu ƴan Najeriya suka riƙa yi ba kan harin bam ga masu Maulidi a Kaduna
- Janar Christopher Musa ya buƙaci ƴan Najeriya da su daina yin kalaman da za su karya gwiwar sojojin ƙasar nan
- Janar Musa ya nanata cewa jefa bam ɗin kuskure ne domin ba za su taɓa kai hari ga ƴan Najeriya da gangan ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bukaci ƴan Najeriya da su yi taka-tsan-tsan da kalamai da ayyukansu domin kada su karya gwiwar sojojin Najeriya.
Da yake magana a yayin shirin Sunrise Daily a gidan talabijin na Channels TV da safiyar Talata, CDS ya sake nanata cewa harin bam da sojojin Najeriya suka kai a ƙauyen Tundun Biri a jihar Kaduna kwanan nan ya faru ne bisa kuskure.
CDS Musa ya bukaci ƴan Najeriya da su fahimci cewa lamarin ba da gangan ba ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Harin Tudun Biri kuskure ne', CDS Musa
A kalamansa:
"Mun fahimci cewa gabaɗaya kowa yana jin ba daɗi. A zahiri muma muna jin ba daɗi. A duk lokacin da muka samu kurakurai, muna amsa kuskuren mu kuma muna jin baƙin ciki sosai game da hakan, musamman idan muka rasa sojojinmu a yaƙi."
"Mu kawai muna son ƴan Najeriya su fahimci cewa lamarin ba da gangan ba ne, ba za mu taɓa kai wa ƴan kasar mu hari da gangan ba. Aikinmu shi ne kare ƴan Najeriya marasa laifi, kuma za mu ci gaba da yin hakan."
"Abin takaici ne cewa a cikin kashi 99% na nasarorin da muka samu, wannan wanda muka samu ya ba mu amsa mara kyau. Amma mun san ƴan Najeriya suna son nasara, muna samun nasara."
Wacce shawara CDS ya ba ƴan Najeriya?
Janar Musa ya bayyana cewa bai kamata ƴan Najeriya su karya gwiwoyin sojojin ba ta hanyar kalaman da suke yi kan harin.
"Na ga mutane da yawa suna magana, yana da sauƙi a gare ku ku ce 'sun yi kuskure', 'ba su yin ƙoƙari', amma menene zaɓin, idan sun janye daga waɗannan wurare, me zai faru? Ba za mu ma samu ƙasa ba." A cewarsa.
"Don haka da har suka zauna, su yi barci a cikin duhu, da rana, da ruwan sama, da kura, da komai, domin tabbatar da cewa ni da ku mun samu damar yin barci, mu yi ayyukanmu na yau da kullum, ina ganin ya kamata mu yaba musu da girmama su."
Manyan Malamai Sun Ziyarci CDS
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugabannin najalisar ƙoli ta shari’a a Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Dr Bashir Aliyu Umar, sun ziyarci babban hafsan tsaron kasa (CDS), Janar Christopher Gwabin Musa, a hedikwatar tsaro da ke Abuja.
A yayin ziyarar, babban hafsan tsaron ya bayyanawa manyan malaman irin jajircewar da rundunar sojojin Najeriya ke yi domin ganin an samu zaman lafiya a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng