Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ya Dauko Hanyar Hana Shoprite Barin Kano
- Babban kantin siya da siyarwa na Shoprite dai ya sanar da aniyarsa na shirin barin jihar Kano a watan Janairu
- Domin dakile wannan shiri, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin zai tattauna da hukummin kamfanin a Abuja
- Jibrin ya ce bai kamata su bar kamfanin ya bar cibiyar kasuwancin arewacin kasar ba a yanzu da ake neman masu zuba hannun jari ta ko'ina
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Kano - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya kammala shirye-shirye don dakile yunkurin Shoprite, daga barin rashenta na jihar Kano, rahoton The Cable.
A makon jiya ne Shoprite ya sanar da hukuncinsa na rufe katafaren kantinsa da ke Ado Bayero Malla a Kano, tare da barin cibiyar kasuwancin a watan Janaiaru.
Kamfanin ya kuma dauka alhakin hakan a kan yanayi da ake ciki na matsin tattalin arziki a yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun bayan fitar da sanarwar, jama'a na ta cece-kuce kan hukuncin rufe kantin wanda aka kafa a Kano a watan Maris din 2014.
Wata sanarwa da mai ba Sanata Barau shawara ta musamman kan harkokin labarai, Ismail Mudashir, ya fitar ya ce mataimakin shugaban majalisar dattawan zai sa labule da hukumomin kamfanin a wannan makon a Abuja kan lamarin, rahoton Daily Trust.
Ya ce:
"Ofishin mataimakin shugaban majalisar dattawa ya shirya matakai don dakile yunkurin Shoprite na ficewa daga jihar Kano. Mai girma mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, CON, zai gana da hukumar kamfanin makon nan inda za a tattauna batun da yiwuwar magance shi.
"Eh batu ne na kasuwanci, amma za mu ga abun da za mu iya yi domin karfafa masu gwiwa su janye hukuncin da suka yanke su ci gaba da zama a Kano.
"Kamar yadda kowa ya sani, akwai dimbin damammaki na kasuwanci a Kano, cibiyar kasuwanci ta Arewacin Najeriya. A lokacin da muke zawarcin masu zzuba hannun jari, ba za mu nade hannayenmu mu barsu su tafi ba."
Shoprite: Sani ya aika sako ga Tinubu
A gefe guda, mun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya tura muhimmin sako ga Shugaba Tinubu kan ‘Shoprite’ a Kano.
Wannan kiran na sanatan na zuwa ne yayin da kamfanin ya shirya barin aiki a jihar Kano, Legit ta tattaro.
Asali: Legit.ng