Tinubu Ya Dauki Mataki Bayan Babban Minista Ya Yi Murabus

Tinubu Ya Dauki Mataki Bayan Babban Minista Ya Yi Murabus

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da murabus ɗin da ministan ƙwadago da samar da ayyuka ya yi daga majalisar ministocinsa
  • Simon Lalong ya yi murabus ne bayan kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da shi a matsayin sanatan Plateau ta Kudu
  • Tsohon gwamnan na jihar Plateau ya zaɓi ya wakilci mazaɓarsa ta Plateau ta Kudu a maimakon cigaba da aiki a gwamnatin Shugaba Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yanke shawarar amincewa da murabus ɗin Simon Lalong, ministan ƙwadago da ayyuka.

Fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da hakan a ranar Litinin, 18 ga watan Disamban 2023.

Tinubu ya amince da murabus din Lalong
Tinubu ya aminta da murabus din Simon Lalong Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Chong Kong Lee
Asali: Facebook

Sylvanus Namang, kakakin jam’iyyar APC a jihar Plateau ya tabbatar da ficewar Lalong daga majalisar zartaswa ta tarayya (FEC), kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi yayin da Wike ya yi abu 1 ana tsaka da rikicinsa da Gwamna Fubara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Lalong ya yi murabus", fadar shugaban kasa ta tabbatar

Jaridar Nigerian Tribune ta ce shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio zai rantsar da jigon na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a cikin wannan makon.

A ranar Litinin, 18 ga watan Disamba, jaridar The Punch ta ruwaito wani mai taimaka wa shugaban ƙasa yana cewa:

"Lalong ya yi murabus. Amma ba a taron FEC ya yi ba, tabbas ya kasance bayan taron ne domin da a ce da farkon taron ne da shugaban ƙasa ko sakataren gwamnatin tarayya sun sanar a lokacin taron."

A halin yanzu, babu tabbas ko har yanzu Lalong zai sake halartar wani taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC).

Lalong ya shiga ruɗani kan barin minista

Ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong, ya bayyana mataki na gaba da zai ɗauka bayan kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da nasararsa a matsayin sanatan Plateau ta Kudu.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya so yin abu 1 kafin rikicinsa da Wike ya yi kamari

Tsohon gwamnan na jihar Filato ya nanata cewa a yanzu haka yana cikin rudani game da ko ya tsaya a matsayin minista a majalisar Tinubu ko kuma ya karbi kujerarsa a majalisar dattawa.

An Fara Dakon Kujerar Lalong

A wani labarin kuma, kun ji cewa an fara dakon kujerar ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong.

Manyan ƴan siyasa daga jihar Plateau na dakon samun kujerar ta ministan Tinubu wanda zai yi murabus ya koma majalisar dattawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng