"Ɗana Ke Siyo Min": An Kama Tsohuwa Mai Shekara 75 Kan Safarar Miyagun Kwayoyi a Legas

"Ɗana Ke Siyo Min": An Kama Tsohuwa Mai Shekara 75 Kan Safarar Miyagun Kwayoyi a Legas

  • Jami'an Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) sun kama wata tsohuwa mai shekara 75, Misis Sekinat Soremekun
  • Misis Seremekun ta yi ikirarin danta ne ke kawo mata haramtattun kayayyakin, kuma NDLEA ta ce dan, Segun, har yanzu ana nemansa
  • A wani lamarin daban a Imo, Jami'an NDLEA sun kama hodar iblis mai nauyin kilogiram 2.287 da aka boye cikin kororon roba kan babban hanyar Owerri-Onitsha

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Legas, Najeriya - Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta kama wata tsohuwa yar shekara 75, Misis Sekinat Soremekun, kan safara haramtattun kwayoyi.

A cikin sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, 17 ga watan Disamba, hukumar ta ce an kama Misis Soremekun a ranar Juma'a, 15 ga watan Disamba.

An kama dattijuwa yar shekara 75 kan sayar da wiwi da kodin a Legas
Dattijuwan da aka kama ta ce danta ne ke kawo mata muggan kwayoyin da ta ke sayarwa. Hoto: @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

"A lokacin da aka kama ta a Oshodi da ke Legas, an gano wasu adadin ganyen wiwi da lita na maganin ruwa na kodin daga hannunta," a cewar wani sashi na sanarwar.

Kara karanta wannan

Abba vs Gawuna: Jigon LP ta bayyana wanda ya kamata Kotun Koli ta ayyana a matsayin gwamnan Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dana shine ya ke siyo wa, in ji Soremekun

Legit Hausa ta tattaro cewa Misis Soremekun ta yi ikirarin cewa danta mai suna Segun, shine ya ke kawo mata haramtattun kwayoyin da ta ke sayarwa.

Hukumar ta NDLEA ta ce a halin yanzu ana neman dan don kama shi.

NDLEA ta kama hodar iblis mai nauyin kilogiram 2.2 a Owerri

A bangare guda, a Imo, Jami'an NDLEA a yayin sintiri kan babban hanyar Owerri zuwa Onitsha, a ranar Alhamis, 14 ga watan Disamba sun kama wani sako dauke da hodar iblis mai nauyin kilogram 2.287.

Sakon ya fito ne daga Legas kuma an boye shi cikin kororon roba, ana hanyar kai shi Fatakwal, babban birnin jihar Rivers.

"Wani da ake zargi, Isaac Okoh, 45, ya riga ya shiga hannu," a cewar sanarwar NDLEA mai dauke da sa hannun Kakakinta Femi Babafemi.

Kara karanta wannan

Babban magana: Obasanjo ya nemi bayar da shaida kan tsohon ministan da EFCC ke nema ruwa a jallo

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164