Dubu Ta Cika: An Kama Wasu Hatsabiban Miyagu da Aka Jima Ana Nema Ruwa a Jallo a Abuja

Dubu Ta Cika: An Kama Wasu Hatsabiban Miyagu da Aka Jima Ana Nema Ruwa a Jallo a Abuja

  • Wasu hatsabiban ƴan fashi da makami uku da yan sanda ke nema ruwa a jallo sun shiga hannu a babban birnin tarayya Abuja
  • Rundunar ƴan sanda ta bayyana sunayen waɗanda aka kama inda ta ce suna da hannu a hare-haren fashi da satar motoci
  • Kwamishinan yan sandan Abuja ya jaddada cewa jami'an rundunar ba zasu yi ƙasa a guiwa ba wajen tsare rayuka da dukiyoyi

FCT Abuja - Rundunar ƴan sanda reshen babban birnin tarayya Abuja ta kama wasu hatsabiban ƴan fashi da makami da ta jima ta nema ruwa a jallo.

Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar yan sandan FCT, SP Josephine Adeh, ita ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Sufeta janar na yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun.
Yan sanda sun kama yan fashi da makami uku da ake zargi a Abuja Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Ta bayyana sunayen waɗanda aka kama bisa zargin aikata manyan fashi da makami, waɗanda suka haɗa da, Gabriel Abba, Sunday Abba, da kuma Abdulkareem Jaffaru.

Kara karanta wannan

Dalibai mata na jami'ar arewa sun kuɓuta daga hannun yan bindiga, VC ya faɗi halin da suke ciki

Yan sanda sun jima suna nemansu

Mutanen uku dai na da alaka da yawaitar fashi da makami, da sace-sacen motoci, da kuma wasu ayyukan laifi na farat ɗaya a cikin babban birnin tarayya Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika waɗanda ake zargin sun jima a cikin jerin hatsabiban da rundunar ƴan sanda ta sa a gaba take nema ruwa jali, a halin yanzu kuma sun shiga hannu.

Vanguard ta ce a sanarwan da kakakin ƴan sandan ta fitar ranar Asabar, 16 ga watan Disamba, 2023, ta ce:

"Wannan samamen ya yi sanadin kwato motoci guda biyu, Toyota Corolla mai launin toka mara lamba da wata bakar mota kirar Toyota Camry 206, ita ma ba ta da lamba da kuma bindigar baretta guda daya."
"A halin yanzu dakarun ƴan sanda sun ci gaba da bincike domin kamo sauran mambobin tawagar fashinsu, waɗanda suka ari na kare."

Kara karanta wannan

Dakarun sojin Najeriya sun ƙara samun babbar nasara kan ƴan bindiga a jihar Sakkwato

"Kwamishinan ƴan sandan Abuja, FCT, CP Haruna G. Garba psc, ya kara tabbatar wa mazauna babban birnin tarayya cewa rundunar ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen samar da tsaro."

CDS ya ce ba wanda za a kyale a harin bam ɗin Kaduna

A wani labarin kun ji cewa CDS Christopher Musa ya jaddada cewa duk sojan da aka gano da laifin a harin ɓam ɗin Kaduna zai gane kurensa.

Babban hafsan hafsoshin tsaron ya ce rundunar soji ba ta ji daɗin kisan da aka yi wa masu Maulidi a kauyen Tudun Biri ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262