Dalibai Mata Na Jami'ar Arewa Sun Kuɓuta Daga Hannun Yan Bindiga, VC Ya Faɗi Halin da Suke Ciki
- A karshe, ɗalibai mata huɗu na jami'ar tarayya ta Dutsinma da suka rage a hannun yan bindiga sun shaƙi iskar 'yanci
- Mataimakin shugaban jami'ar, Farfesa Armaya’u Hamisu-Bichi, ne ya tabbatar da haka a Katsina, ya faɗi mataki na gaba
- Tun ranar 3 ga watan Oktoba, mahara suka sace ɗalibai biyar daga gidan kwanan su amma daga bisani ɗaya ta gudo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Hukumar jami'ar tarayya da ke garin Dutsin-ma a jihar Katsina ta ce ragowar ɗalibanta mata huɗu da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su sun shaƙi iskar ƴanci.
Mataimakin shugaban jami'ar (VC), Farfesa Armaya’u Hamisu-Bichi, shi ne ya tabbatar da haka yayin zantawa da ƴan jarida a Katsina ranar Jumu'a, 15 ga watan Disamba.
Ya bayyana cewa ɗaliban guda huɗu da Allah ya sa suka tsira a yanzu, suna daga cikin ɗalibai biyar da ƴan bindiga suka sace kwanakin baya, jaridar Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan baku manta ba, mahara sun yi awon gaba da ɗaliban ranar 3 ga watan Oktoba, 2023 a gidan da suke zaune na haya da ke bayan makarantar Mariyamu Ajiri memorial school a Dutsinma.
Wane hali ɗaliban ke ciki bayan sun kuɓuta?
Shugaban jami'ar ya ƙara da bayanin cewa ɗaliban da suka kubuta a halin yanzu za a duba lafiyarsu a asibiti gabanin miƙa su ga danginsu, rahoton Leadership.
Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta tuno yadda rundunar ƴan sanda ta tabbatar da cewa ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai mata 5 na jami'ar tarayya ta Dustinma a watan Oktoba.
Haka nan kuma a ranar 20 ga watan Oktoba, 2023, ƴan sanda suka sake tabbatar da cewa ɗaya daga cikin ɗaliban ta yi nasarar gudowa daga hannun masu garkuwa.
Legit Hausa ta fahimci cewa har yanzu akwai ragowar ɗaliban jami'ar Gusau da ke hannun ƴan bindiga tun bayan sace su daga gidajen kwanan su.
Jerin Jami'o'in Addinin Musulunci 5 Da Ya Kamata Ku a Sani
Kuna da labarin Akwai Jami'o'in Musulunci da dama da aka kafa a Najeriya da nufin samar da ingantaccen ilimi bisa tsarin addinin musulunci.
Manufar kafa irin waɗannan jami'o'in ita ce samar da mahallin da dalibai za su iya koyan darussa iri-iri tare da samun zurfin fahimtar shari'a da dabi'un addinin Musulunci.
Asali: Legit.ng