Olusimbo Ige: Yar Najeriya Ta Zama Bakar Fata ta Farko a Matsayin Kwamishinar Lafiya ta Chicago

Olusimbo Ige: Yar Najeriya Ta Zama Bakar Fata ta Farko a Matsayin Kwamishinar Lafiya ta Chicago

  • Kasar Najeriya ta sake kafa tarihi bayan nadin Olusimbo Ige a matsayin kwamishinar sashen kula da lafiyar jama'a na Chicago
  • Nadin Dr Ige ya sa ta zama fakar fata mace ta farko da aka taba nadawa kan babban mukami a tarihin sashen
  • An tattaro cewa Mayor Brandon Johnson ne ya amince da nadin Dr Ige bayan tsige Dr Allison Arwady

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata yar Najeriya, Dr Olusimbo Ige, ta kama aiki a matsayin kwamishina a sashen kula da lafiyar jama'a na Chicago a kasar Amurka.

Nadin nata ya sa ta zama bakar fata mace ta farko da ta samu wannan mukami a tarihin sashen.

Yar Najeriya ta zama bakar fata mace ta farko
Olusimbo Ige: Yar Najeriya Ta Zama Bakar Fata ta Farko a Matsayin Kwamishinar Lafiya ta Chicago Hoto: NYAM
Asali: UGC

A wata wallafa da ta yi a soshiyal midiya, tsohuwar yar majalisa kuma shugabar hukumar NiDCOM, Abike Dabiri, ta taya Ms Olusimbo murna kan wannan mataki da ta kai a rayuwa.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Gobara ta kama ofishin gwamnan jihar Borno

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta rubuta:

"An kafa tarihi! Ina taya bakar fata mace ta farko da aka nata a matsayin kwamishina a tarihin sashen kula da lafiyar jama'a na Chicago yar Najeriya kuma Ba'amurkiya. Ina taya Dr. Olusimbo Ige murna."

Yadda Mayor Brandon Johnson ya zabi Dr Ige

A halin da ake ciki kuma, nadin Olusimbo ya biyo bayan korar da aka yi wa tsohuwar kwamishinan, Dr Allison Arwady ba zato ba tsammani.

Kamar yadda kafar yada labarai ta CBS ta rahoto, an kori Dr Arwady ne watanni uku bayan da aka nada ta a kan babban mukamin.

Bayan korar ta, Mayor Brandon Johnson ya sanar da nadin Dr Olusimbo a matsayin wacce za ta gaje ta.

Mayor Johnson ya ce:

"Dr. Ige babban karin ci gaba ce ba wai ga gwamnatinmu ba kawai, harma ga birnin Chicago."

Kara karanta wannan

Sanusi ga ECOWAS: Ba a Sa Takunkumi ga Israila ba, Amma Kun Hana Nijar Abinci da Lantarki

A baya Simbo ta kasance manajan daraktan shirye-shirye a Gidauniyar Robert Wood Johnson, wata kungiyar kiwon lafiyar jama'a mai zaman kanta ta New Jersey.

Ta kuma yi aiki a matsayin mataimakiyar kwamishina na Ma'aikatar Lafiya da lafiyar kwakwalwa na birnin New York.

Yar Najeriya ta zama likita a UK

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata mata yar Najeriya mai suna Odocha Sylvia ta shawarci mutanen da ke niyan komawa birnin UK da su kasance masu hakuri.

Sylvia ta ba da labarin kanta domin karfafawa jama'a gwiwa da kuma koyar da su muhimmanci hakuri da juriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng