Wata Sabuwa: Ana Zargin Shugaba Tinubu da Rura Wutar Rikici a Jihar PDP, Bayani Sun Fito

Wata Sabuwa: Ana Zargin Shugaba Tinubu da Rura Wutar Rikici a Jihar PDP, Bayani Sun Fito

  • Ƙungiyar kabilar Ijaw ta ƙasa (INC) ta ce Bola Tinubu ya yi shiru game da rikicin da ministan Abuja ya tayar a Ribas saboda yana goyon bayansa
  • Shugaban INC na kasa, Farfesa Benjamin Okoba, ya bayyana cewa duk wani cin mutunci da aka yi wa Gwamna Fubara ya shafi ƙasar Ijaw
  • Okaba ya ce mutanen ƙabilar Ijaw sun fusata kuma ba zasu lamurci duk wani yunkurin na tsige Fubara daga kujerar gwamna ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Fatakwal, jihar Ribas - Ijaw National Congress (INC) ta zargi Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da goyon bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike a rikicin siyasar da ya ɓarke a jihar Ribas.

Shugaban ƙungiyar ƴan kabilar Ijawa ta ƙasa INC, Farfesa Benjamin Okaba ya yi zargin cewa Tinubu ya rungume hannu, ya ki jan kunnen Wike kan rikicinsa da Gwamna Siminalayi Fubara.

Kara karanta wannan

Wike ya shiga matsala yayin da ake zarginsa da aikata wani mummunan laifi

Ana zargin Tinubu da rura wutar rikicin siyasar Ribas.
Rivers: Kungiyar Ijaw ta zargi Shugaba Bola Tinubu ya rura wutar rikicin Wike da Fubara Hoto: Nyesom Wike/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Farfesa Okaba ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da ƴan jarida a gidan gwamnati da ke Fatakwal ranar Jumu'a, 15 ga watan Disamba, 2023, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma jagoranci ɗaruruwan ƴan kabilar Ijaw sun gudanar da tattakin nuna goyon baya ga Gwamna Fubara.

INC ba za ta yarda a tsige Gwamna Fubara ba

A kalamansa, Okaba ya ce:

"Amma ganin yadda (Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu) ya yi gum da bakinsa ya nuna cewa yana goyon bayansa, kuma mu ba za mu lamurci haka ba."
"A yanzu da nake magana mutanen mu sun zo wuya a fusace suke ta yadda ba zamu iya tabbatar da mai zai faru ba idan abubuwa suka ci gaba da tafiya a haka."

Okaba ya ce al’ummar Ijaw sun fusata ne kan yadda aka mayar da kabilarsu saniyar ware, kuma ba za su bar duk wani yunkuri na siyasa da zai tsige Fubara daga mukaminsa ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya maida zazzafan martani yayin da ake shirin tsige shi daga kan mulki

A rahoton Daily Post, ya kara da cewa:

“Mutanen Ijaw miliyan 40 sun fusata kuma sun kawo wuya, suna cewa zage-zagen da aka yi wa Gwamna Fubara, tamkar cin mutunci ne ga daukacin ƴan ƙabilar Ijaw."

Ministan Abuja ya shiga wata sabuwar matsala

A wani rahoton kuma kun ji cewa Rigingimun da suka dabaibaye Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, sun ƙara ɗaukar zafi

Ana zargin tsohon gwamnan na jihar Rivers cewa ya kitsa kisan wani babban jami'in ƴan sanda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262