Gwamnan APC Ya Gargadi Masu Rike da Mukaman Siyasa Kan Abu 1
- Gwamnan jihar Nasarawa ba ya son aiki da mutanen da ba su biyayya ga gwamnatinsa duk da suna cikinta
- Gwamna Abdullahi Sule ya gargaɗi masu riƙe da muƙamai a gwamnatinsa waɗanda ke yi wa wasu biyayya da su yi murabus
- A cewar gwamnan duk wanda ya samu cewa biyayyarsa ba ta tare da gwamnatinsa, to zai rasa muƙaminsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya gargaɗi masu rike da muƙaman siyasa marasa biyayya da su sauya hali ko kuma ya kore su daga gwamnatinsa.
Da yake jawabi yayin wata ganawa da ya yi da waɗanda ya naɗa muƙamai a gidan gwamnati da ke Lafia a jiya Juma'a, gwamnan ya ce waɗanda ke da niyya mara kyau bai kamata su kasance a cikin gwamnati ba, cewar rahoton Leadership.
Sule dai kafin yaƙin neman zaɓen 2023 ya yi irin wannan gargaɗin ga waɗanda aka naɗan muƙamai waɗanda ake ganin suna biyayya ga wasu mutane a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamansa:
"Ba na son korar kowa. Na yi imanin cewa yana da muhimmanci da farko mu tambayi mutane saboda girmamawa ko dai su canza hanyoyinsu su zama masu biyayya ga gwamnati ko kuma su bar gwamnati."
"Abin da mutum mai ƙima daraja zai yi, idan ba na biyayya ga mutum babu dalilin yin aiki a ƙarƙashin wannan mutumin. Idan kana tunanin biyayyarka ba ta ga gwamnati, dan Allah ka zama mutum ka yi murabus."
Gwamnan na sane da ƙulla-ƙullar da ake masa
Gwamnan ya ce yana sane da taron dangin da aka yi masa a lokacin zaɓen gwamna, inda ya ce duk da cewa ya yi ƙoƙarin haƙura da cin amanar da aka yi masa a lokacin zaɓe da kuma rikicin da ya biyo bayan zaɓen, har yanzu lamarin ya ci tura.
A kalamansa:
"Mun yi ƙoƙarin kawar da kai a lokaci mai wuya na zaɓe da na rigingimun bayan zaɓe. Ina son na gaya muku ba tare da tantama ba cewa ba za mu lamunci rashin biyayya ga wannan gwamnatin ba. Mutanen da su ke biyayya ga wasu ba za su yi aiki da wannan gwamnatin ba."
Ya kuma yi gargaɗin cewa gwamnatinsa ba za ta kara amincewa da rashin jituwa tsakanin matakai daban-daban da masu riƙe da muƙaman siyasa ba, yayin da ya bukace su da su hada kai domin amfanin jihar da al’ummarta.
Majalisar Dokokin Nasarawa Ta Yi Sabbin Nade-Nade
A wani labarin kuma, kun ji cewa sabon kakakin malisar jihar Nasarawa, Danladi Jatau ya sanar da nadin wasu manyan mukamai guda uku a zauren majalisar.
Sabbin nade-naden da aka yi sun hada da Suleiman Yakubu Azara daga mazabar Awe ta Kudu karkashin APC matsayin shugaban masu rinjaye na majalisar.
Asali: Legit.ng