Nnamdi Kanu: Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Makomar Shugaban Kungiyar Ta'addanci IPOB
- Kotun koli ta yi fatali da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara wadda ta sallami tare da wanke jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu
- Bisa wannan hukunci, yanzu Kanu zai fuskanci shari'a kan tuhumar cin amanar kasa da ayyukan ta'addanci
- A cewar kotun koli, ba wanda zai taso ƙeyar shugaban IPOB zuwa Najeriya idan da tun farko bai tsallake sharuddan beli ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Kotun kolin Najeriya ta yi watsi hukuncin kotun ɗaukaka ƙara wanda ya bada umarnin a saki jagoran ƙungiyar ƴan aware IPOB, Nnamdi Kanu, cewar The Nation.
A cewar kotun ƙoli tabbas an saɓa doka wajen taso keyar Kanu daga Kenya zuwa Najeriya bayan ya tsallake sharuɗɗan beli amma hakan ba zata faru ba da ace bai gudu ba.
Bisa haka kotun mai daraja ta ɗaya a Najeriya ta jingine hukuncin bada belinsa, kana ta amince a ci gaba da tuhumar Kanu kan ƙarar zargin hannu a ayyukan ta'addanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun da farko, Gwamnatin tarayya ta bukaci kotun da ta yi watsi da hukuncin kotun daukaka kara, wadda ta kori zargin cin amanar kasa da ake yi wa shugaban kungiyar IPOB.
Lauyan gwamnati, Tijani Gazali, ya roƙi kotun kolu ta tabbatar da hukuncin babbar kotun tarayya, wacce ta yanke cewa dole Kanu ya fuskanci shari'a kan tuhumar da ake masa.
Lauyan Kanu ya faɗi abinda ya sa suke son a wanke shi
A nasa bangaren, Kanu ya roki kotun koli da ta amince da hukuncin kotun daukaka kara tare da tabbatar da sallamarsa da kuma wanke shi daga tuhuma.
Mike Ozekhome, Lauyan Nnamdi Kanu, ya bukaci kotun kolin ta kori karar gwamnatin tarayya kuma ta ci FG tara mai tsoka bisa ja da hukuncin kotun ɗaukaka kara.
Ya kuma roƙi kotun ta amince da bukatar wanda yake karewa, yana mai cewa Kanu ya kasance a tsare tun shekarar 2021, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Daga ƙarshe kotun kolin ta bayar da umarnin Kanu ya je ya kare kansa a sauran tuhume-tuhume bakwai na ta’addanci a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Kotu ta ce a rataye matashin da ya kashe mahaifiyarsa
A wani rahoton na daban Babbar jojin jihar Niger ta yake hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani matashi da ya kashe mahaifiyarsa ta hanyar cinna mata wuta.
A watan Disamba 2021 ne matashin mai suna Stephen Jiya ya kashe mahaifiyarsa mai shekaru 61 bisa zarginta da silar bacewar matarsa a Suleja.
Asali: Legit.ng