Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Mutumin da Ya Cinnawa Mahaifiyarsa Wuta
- Babbar jojin jihar Niger ya yake hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani matashi da ya kashe mahaifiyarsa ta hanyar cinna mata wuta
- A watan Disamba 2021 ne matashin mai suna Stephen Jiya ya kashe mahaifiyarsa mai shekaru 61 bisa zarginta da silar bacewar matarsa a Suleja
- A ranar 23 ga watan Nuwamba, 2022 ne aka fara shari'ar Jiya bayan gurfanar da shi gaban mai shari'ar a ranar 14 ga watan Satumba, 2022
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Niger - Kotu ta yanke wa wani matashi dan shekaru 39, Stephen Jiya hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kama shi da laifin cinnawa mahaifiyarsa wuta har ta mutu a cikin watan Disamba 2021.
Jiya ya kashe mahaifiyarsa mai shekaru 61, Mrs Comfort Jiya, wata tsohuwar darakta a ma'aikatar ilimi ta jihar Niger kan zarginta da silar bacewar matarsa a Suleja.
Dokar da ta yanke hukuncin kisa kan Stephen Jiya
Premimun Times ta ruwaito babbar jojin jihar Niger, Mai Shari'a Halima Ibrahim Abdulmalik, wacce ta yanke hukunci kan Jiya, ta ce ta same shi da laifin kisan kai karkashin sashe na 221 da ke a kundin dokar final.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gurfanar da Jiya gaban babban jojin a ranar 14 ga watan Satumba, 2022, yayin da aka fara sauraron shari'ar ta sa a ranar 23 ga watan Nuwamba, 2022, rahoton The Nation.
Kotu ta garkame lebura wata bakwai kan laifin satar agwagin turawa
A wani labarin, wata kotu mai zamanta a Jos, babban birnin jihar Filato ta yanke hukuncin zaman gidan kaso na wata bakwai kan Andrew Enoch bayan samunsa da laifin satar agwagin turawa guda uku.
Enoch ya amsa laifin satar agwagin, wanda ya ba Mai Shari'a Anas Mohammed damar aike da matashin gidan gyaran halin, amma da zabin biyan tara, Legit Hausa ta ruwaito.
Duk da ba matashin damar biyan tarar Naira dubu 70, kotun ta kuma umurci Enoch ya biya matar da ya satarwa agwagin Naira dubu 90 ko ya kara watanni a gidan yarin.
Tun da fari dai jami'i mai shigar da kara, Sifeta Labaran Ahmed, ya shaidawa kotun cewa wani Ishaiah Habi ne ya kai karar wanda ake zargin ofishin 'yan sanda a ranar 17 ga watan Agusta.
Asali: Legit.ng