Kirsimeti: Attajirin Dan Kasuwa Na Shirin Raba Buhunan Shinkafa 1000, Shanu 5 da Man Gyada
- Wani matashi dan Najeriya ya shirya yi wa mutane tagomashin alkhairi a yayin bukukuwan Kirsimeti
- Mutumin mai suna Mr Blord a Instagram, ya ce zai raba buhunan shinkafa 1,000 jarkokin man gyada da shanu biyar
- Ya yada wani bidiyo a Instagram wanda ke nuna buhunan shinkafa yayin da yake shirin raba kyautar
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wani matashi dan Najeriya na shirin raba buhunan shinkafa 1000 don taimakawa talakawa yayin bukukuwan Kirsimeti.
Attajirin dan kasuwar mai suna Mr Blord ya nuna karara cewa wannan al'adarsa duk shekara rabawa mutane abinci.
Ya ce baya ga buhunan shinkafa 1000 wanda ya nuna a bidiyon, zai kum raba jarkokin man gyada 1000.
"Zamani ya canza" Shugaban JAMB ya faɗa wa ɗalibai yadda zasu samu aiki bayan gama digiri a Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mr Blord ya kuma ce zai rabawa mutane shanu biyar domin su yanka su yi bukukuwan.
Attajiri zai rabawa mutane buhunan shinkafa 1000 a Ebenebe, jihar Anambra
Bord ya ce zai raba shinkafa da sauran kayan abinci a mahaifarsa, Ebenebe, jihar Anambra.
"Kyautar buhunan shinkafa 1,000 a Ebenebe, shanu 5, man gyada jarka 1k, Allah ya albarkaci mutanen Anambra, Allah ya albarkaci mutanen Ebenebe. Ina alfahari da mutanena, don Allah a taya Blord da addu'a a kowace safiya, mun san abubuwa sun yi wuya, amma jama'ata za su yi murmushi a wannan Kirsimetin da sabuwar shekara, na gode wa dukkan abokan cinikinmu, muna matukar godiya da kuka ba mu wannan kudi, idan ba ku yi ciniki ba ba za mu sami wannan kudaden ba, ina godiya gareku."
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun jinjinawa Blord
@charlesofgoodlife ya yi martani:
"Mutanen Anambra sun iya kyauta, shine dalilin da yasa muke samun ci gaba."
@diplomaticjaykay ya ce:
"Gwamnatin tarayya bata yi ya wuce haka ba faa. Blord saboda wani dalili."
@jentlechiefo ya ce:
"Allah ya albarkace ka kan yiwa mutanenka kyauta."
Bidiyon dan Najeriya yana sharholiya
A wani labarin, mun ji cewa wani bidiyo mai ban dariya na wani dan Najeriya a gidan cin abinci ya bar mutane cikin mamaki a TikTok.
Bidiyon ya nuno matashin yana shan askirin da cincin a wani wajen cin abinci inda ya mayar da hankalinsa kacokan a kansu.
Asali: Legit.ng