Bakin Ciki Yayin Da Tsohon Gwamnan Anambra, Ezeife, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Tsohon gwamnan jihar Anambra, Chukwuemeka Ezeife, ya rasu a ranar Alhamis a Cibiyar lafiya na Tarayya da ke Abuja yana shekara 85
- Cif Rob Ezeife, a madadin iyalan, ya sanar da rasuwar tsohon sakataren dindindin din na tarayya a safiyar ranar Juma'a
- A cewar Rob, za a sanar da al'umma shirye-shiryen jana'izar marigayin dan siyasan nan ba da dedewa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Anambra, Dakta Chukwuemeka Ezeife, ya riga mu gidan gaskiya.
A cewar The Punch, tsohon gwamnan ya rasu ne a Cibiyar Lafiya na Tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda tsohon gwamnan na Anambra ya rasu
An bayyana rasuwarsa cikin wata takaitaccen sanarwar manema labarai da aka fitar a ranar Juma'a da safe, 15 ga watan Disamba mai dauke da sa hannun Cif Rob Ezeife a madadin iyalin.
Marigayin wanda aka fi kira da 'Okwadike' ya yi gwamna a Anambra daga Janairun 1992 zuwa Nuwamban 1993 lokacin Jamhuriya ta uku da aka datse ta, The Punch ta rahoto.
An haife Ezeife ne a ranar 20 ga watan Nuwamban 1938.
Sanarwar kamar yadda The Cable ta rahoto ta ce:
"A madadin Iyalan Ezeife na Igbo-Ukwu, ina son sanar da rasuwar babban dan mu, 'Okwadike', Dakta Chukwuemeka Ezeife, CON, tsohon sakataren dindindin, tsohon gwamnan Jihar Anambra, tsohon mashawarcin shugaban kasa kuma tsohon mai neman takarar shugaban kasa.
"Abin bakin cikin ya faru ne jiya misalin karfe 6 na yamma a Cibiyar Lafiya, Abuja.
"Za a fitar da karin bayani dangane da marigayin da shirye-shiryen birne shi nan gaba."
Shehu Othman ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 91
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar tsohon kwamishina na tsohuwar jihar Benue, Alhaji Shehu Othman, ya rasu ne yana da shekaru 91 a duniya.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Othman ya mutu ne a ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba, a Asibitin Trust Charitos da ke garin Jabi a Abuja, bayan gajeruwar rashin lafiya.
Iyalan Othman suma sun tabbatar da rasuwarsa cikin wata sanarwa da ke nuna za a birne dan siyasan a ranar Juma'a bayan sallar Azahar a babban Masallacin Abuja.
Asali: Legit.ng