Allah Ya Yi Wa Shehu Othman Rasuwa Yana Da Shekara 91

Allah Ya Yi Wa Shehu Othman Rasuwa Yana Da Shekara 91

  • Iyalan tsohon kwamishinan jihar Benue, Alhaji Shehu Othman, sun shiga gagarumin jimami sakamakon rasuwarsa
  • Iyalansa sun tabbatar da lamarin cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba, suna mai cewa ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya
  • Marigayin ya rike mukamai da dama a gwamnatin tsohuwa jihar Benue-Plateau, da kuma wasu mukaman a hukumomin tarayya daban-daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

FCT, Abuja - An tabbatar da rasuwar tsohon kwamishina a tsohuwar jihar Benue, Alhaji Shehu Othman. Dan siyasan ya rasu yana da shekaru 91 a duniya.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, Othman ya rasu a ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba, a Asibitin Trust Charitos da ke Jabi, a Abuja bayan gajeruwar rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Yanzu: Bakin ciki yayin da tsohon Gwamnan Anambra, Ezeife, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Shehu Othman
Najeriya ta yi rashin wani babban dan siyasa, Shehu Othman. Hoto: Shehu Othman
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Iyalan Othman sun tabbatar da rasuwarsa cikin wata sanarwa suka kuma nuna cewa za a birne dan siyasan a ranar da ya rasu bayan sallar azahar a Babban Masallacin Abuja.

Iyalan sun rubuta:

"Inna lillahi wa ina ilaihi raji un.
"Za a yi jana'iza bayan sallar Azahar (1.30pm) a Masallacin Kasa na Abuja.
"Sannan za a birne shi a Makabartar Gudu bayan masa sallah."

An haifi Othman ne a ranar 26 ga watan Yuni, kuma shi da ke sarautar Magajin Garin Keana kafin rasuwarsa.

Malami a OAU ya fadi matacce a ofishinsa

Tunda farko, Legit ta rahoto cewa wani lakcara a Jami'ar Obafemi Awolowo (OAU) da ke Ile-Ife a jihar Osun ya fadi ya kuma ce ga garinku a ofishinsa, jaridar The Sun ta rahoto.

Marigayin, wanda aka ce sunansa Dr Ayo Ojediran, ya koyar a Sashin Kimiyya da Fasahar Ilimi, Tsangayar Ilimi a makarantar.

Kara karanta wannan

Jerin mutane 8 da suka bada taimakon miliyan 700 da aka kashe masu Maulidi a Tudun Biri a Kaduna

An tsinci gawar malamin a ofishinsa a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba, yayin da wasu abokan aikinsa suka shiga ofishin.

Tsohon minista Musa Gwadabe ya rasu

A wani rahoton kun ji cewa tsohon Ministan Kwadago kuma jigo a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Musa Gwadabe ya riga mu gidan gaskiya.

Rahotanni sun bayyana cewa Gwadabe ya rasu a ranar Laraba 26 ga watan Afrilu yayin da ya ke da shekaru 87 a duniya. Ya mutu bayan gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel