"Zamani Ya Canza" Shugaban JAMB Ya Faɗa Wa Ɗalibai Yadda Zasu Samu Aiki Bayan Gama Digiri a Najeriya

"Zamani Ya Canza" Shugaban JAMB Ya Faɗa Wa Ɗalibai Yadda Zasu Samu Aiki Bayan Gama Digiri a Najeriya

  • Shugaban JAMB ya buƙaci yan Najeriya su daina dogara cewa digiri zai sa su samu aiki a Najeriya a wannan zamanin
  • Farfesa Ishaq Oloyede ya ce zamani ya canza, ba a buƙatar karatu a takarda, an fi kallon abinda zaka iya aikatawa
  • A cewarsa, akwai ayyuka da dama da ke kan siraɗin bacewa saboda yanayin canzawar zamani

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB), Farfesa Ishaq Oloyede, ya ce zamani ya sauya kan samun aiki da kwalin digiri.

Shugaban JAMB ya ce takardar shaidar kammala karatun jami'a a zamanin da aka shigo yanzu, ba zata samar maka da aikin yi ba a kasar nan.

Kara karanta wannan

Daga Ƙarshe, Gwamnan PDP ya bayyana wanda zai marawa baya a zaben mai zuwa 2024

Shugaban JAMB ya gargaɗi dalibai kan sauyin da aka samu a duniya.
Kwalin Digiri Kadai Ba Zai Sa Ka Samu Aiki Ba a Najeriya, Shugaban JAMB Hoto: JAMB
Asali: Twitter

Maimakon digaro da kwalin digiri, Farfesa Oloyede, ya bukaci ɗalibai da su bada fifiko kuma su maida hankali wajen samun kwarewa a wasu fannoni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, a yanzu kwarewa da zama gwani wajen yin aiki shi ne abu mai muhimmanci, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi wannan jawabi ne a garin Malete da ke Jihar Kwara a ranar Alhamis yayin da yake gabatar da lakcar taron yaye ɗalibai a Jami’ar Jihar Kwara (KWASU) ranar Alhamis.

Abin da ya kamata ɗalibai su ba muhimmanci - Oloyede

Oloyede, Farfesa a fannin Islam, ya bukaci 'yan Najeriya da su shirya fuskantar kowane irin kalubale na zamani ta hanyar ɗaukar koyon abubuwan rayuwa da mahimmanci.

Ya jaddada cewa, "koyon ilimi kaɗai ba shi da amfani idan ba zaka yi aiki da shi ba," inda ya ƙara da cewa, "karatu shi ne samun sabbin fasahohi, ilimi da hangen nesa."

Kara karanta wannan

"Ainahin dalilin da yasa muka tsige gwamna da yan majalisar PDP 16": Alkalin kotun daukaka kara

"Waɗanda ke karatu, su juya wani fannin su ƙara karatu suke samun nasara a rayuwa, amma waɗanda ba su da tunanin sake gwada sa'arsu a haka zasu kare cikin baƙin ciki."

Shugaban JAMB ya ci gaba da cewa:

"Duniyar da muke ciki yanzun ta sha bamban da zamanin kakannin mu, ɗaya daga cikin abubuwan da suka kawo sauyi shi ne bayanai, wanda ke kara haɓaka, fasaha na karuwa."
"Sauye-sauyen da aka samu wasu damarmaki ne da barazana domin ayyukan da ake da su kamar rubutu, ƙarban baki, sarrafa kwanfuta, aikin tafiye-tafiye da sauransu na dab da ɓacewa."

Farfesa Oloyede ya shawarci daliban da suka kammala karatun su tuna cewa karatu da kwarewa da kuma ilmantarwa sune tushen da za su taimake su a duniyar nan, Vanguard ta rahoto.

Yan majisa 26 sun yi zama a jihar Ribas

A wani rahoton na daban Mambobi 26 na majalisar dokokin jihar Ribas sun yi zama a ɗakin taro na rukunin gidajen ƴan majalisu ranar Alhamis.

Wannan zama na zuwa ne kwana ɗaya bayan Gwamna Fubara ya sa an rushe zauren majalisar dokokin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262