Tinubu Ya Kubalanci Bankin Duniya Kan Cire Tallafin Mai, Ya Fadi Alfanun da Ya Samu

Tinubu Ya Kubalanci Bankin Duniya Kan Cire Tallafin Mai, Ya Fadi Alfanun da Ya Samu

  • Gwamnatin Tarayya ta yi martani kan kalaman Bankin Duniya kan biyan kudaden tallafin mai a kasar
  • Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya ce babu maganar tallafi ya tafi kenan har abada ba zai dawo ba
  • Wannan na zuwa ne bayan Bankin ya zargi gwamnatin da ci gaba da biyan kudaden tallafin mai a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta kalubalanci Bankin Duniya kan martani game da cire tallafin man fetur a kasar.

Gwamnatin ta ce har yanzu babu maganar dawo da tallafi, ya tafi kenan har abada inda ta ce ba a biyan kudin tallafi a kasar.

Tinubu ya kalubalanci Bankin Duniya kan cire tallafin mai a Najeriya
Tinubu ya yi martani kan kalaman Bankin Duniya kan tallafin mai. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Wane martani Tinubu ya yi ga Bankin Duniya?

Kara karanta wannan

An ga tashin hankali bayan gini ya ruguje kan mata da jaririnta mai kwanaki 9, mijin ya shiga yanayi

Ministan yada labarai, Idris Mohammed shi ya bayyana haka a yau Alhamis 14 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idris ya ce kamar yadda Bola Tinubu ya yi alkawari tun hawanshi mulki ba zai iya ci da biyan kudaden tallafi ba, cewar TheCable.

Ya ce a dalilin cire tallafin mai a kasar an samu karin shigar kudade zuwa asusun Gwamnatin Tarayya wanda ba a saba gani ba.

Mene Bankin Duniya ke cewa kan tallafin?

A jiya Laraba ce 13 ga watan Disamba Bankin Duniya ya ce yadda farashin mai ke kara tsada watakila gwamnatin na ci gaba da biyan kudaden.

Bankin ya ce ya kamata 'yan kasar su rinka siyan litar a kan kudi naira 750 madadin 650 da ake siyarwa a wasu wurare, cewar Daily Trust.

Yayin martaninshi, Ministan ya ce tuni su ka soke ci gaba da biyan kudaden tallafin mai a kasar tun bayan hawan Shugaba Tinubu mulki.

Kara karanta wannan

Bankin duniya ya fasa kwai, ya fadi farashin da ya kamata a saida fetur a gidajen Mai

Ya ce:

"Biyan kudin tallafi ya wuce har abada kamar yadda Tinubu ya sanar a ranar kama aiki akan ba zai iya biyan kudaden ba.
"Mu na samun makudan kudade ne saboda cire tallafin, ba za a sake dawo da shi ba, ya tafi kenan kuma shi ke kara mana kudin shiga."

Bankin Duniya ya yi martani kan cire tallafi

A wani labarin, Bankin Duniya ya bayyana cewa bai kamata ana siyan litar mai 650 ba a Najeriya.

Bankin ya ce ya kamata ace litar mai ta kai naira 750 a fadin kasar inda ya ce watakila har yanzu gwamnatin na biyan kudin tallafi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.