“Ina da Tarin Ilimi”: Tsohon Shugaban Daliban Jami’ar UNIBEN Ya Tsaya Takarar Gwamna a Jihar Edo

“Ina da Tarin Ilimi”: Tsohon Shugaban Daliban Jami’ar UNIBEN Ya Tsaya Takarar Gwamna a Jihar Edo

  • Aka ce mutum ba zai iya gane karfinsa ba har sai ya gwada yin fada da giwa, kamar haka dai wani tsohon shugaban dalibai ya fito takarar gwamna a Edo
  • Mr Michael Oshiobuhie ya jaddada kudirinsa na kawo ci gaba a jihar Edo ma damar aka bashi dama, saboda tarin iliminsa a fannin injiniyanci
  • Jam'iyyar LP wacce Mr Oshiobuhie ya tsaya takara karkashinta, ta yi masa fatan alkairi yayin da jihar ke fuskantar zaben gwamna a shekarar 2024

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Edo - Wani tsohon shugaban kungiyar daliban jami'ar Benin, Michael Oshiobuhie ya fito takarar gwamnan jihar Edo karkashin jam'iyyar LP a zaben jihar na 2024 da ke matsowa.

Kara karanta wannan

Edo: Ana shirin zaben gwamna a 2024, ɗan takara ya yi murabus, ya fice daga jam'iyyar adawa

Oshiobuhie wanda ya karanci injiniyanci ya isa sakatariyar jam'iyyar da ke Benin a ranar Laraba, domin bayyana kudirinsa a hukumance tare da fatan samun goyon bayan jam'iyyar.

Michael Oshiobuhie ya tsaya takarar gwamnan jihar Edo
Mr Oshiobugie ya ce idan ya zama gwamna, zan yi amfani da kwarewarsa wajen bunkasa amfani da iskar gas a jihar. Hoto: @engrosho
Asali: Facebook

"Ina da tarin ilimi," Mr Oshiobugie ya fadi dalilin tsayawa takara

A shekarar 1996 ne Oshiobugie ya shugabanci kungiyar SUG a jami'ar UNIBEN, ya ce yana da duk wata kwarewa da ake bukata don shugabantar jihar Edo, jaridar The Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

"Ina da ilimi mai zurfi kan injiniyanci, wanda ake bukata a Najeriya yanzu, akwai bukatar wanda zai farfado da tattalin arziki wanda ina da kwarewa akan hakan.
"Idan har na zama gwamna, zan yi amfani da kwarewa ta wajen alkinta ma'adan jihar da suka shafi iskar gas, zan tabbatar tattalin arziki ya amfani daga sarrafa gas a Edo."

The Guardian ta ruwaito shugaban jam'iyyar LP na jihar, Kelly Ogbaloi, na cewa:

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta fatattaki shugaban karamar hukuma a jihar Niger, ta fadi dalili

"Kamar kowanne dan takara, jam'iyyar ta karbi Oshiobugi hannu biyu tare da yi masa fatan alkairi."

EFCC na neman tsohon ministan Najeriya ruwa a jallo

A wani labarin kuma, hukumar EFCC ta baza komar kama wani tsohon ministan makamashi da wutar lantarki a zamanin mulkin Obasanjo kan zargin karkatar da kudin kwangila.

Hukumar na zargin Mr Olu Agunloye da handame dalar Amurka biliyan shida na kwangilar tashar wutar lantarki ta mambila, da tsohon Shugaba Obasanjo ya ba ma'aikatar makamashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.