'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Hedkwatar Ƙaramar Hukuma a Arewa, Sun Tafka Mummunar Ɓarna

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Hedkwatar Ƙaramar Hukuma a Arewa, Sun Tafka Mummunar Ɓarna

  • Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 10 yayin da suka kai sabon harin hedkwatar ƙaramar hukumar Zurmi a Zamfara
  • Mazauna garin sun bayyana yadda ƴan ta'addan suka shiga garin da yamma, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi
  • Har yanzun rundunar yan sanda ba ta ce komai ba kan sabon harin wanda sojoji suka yi kokarin daƙile wa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai sabon hari kan mazauna garin Zurmi, hedkwatar ƙaramar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, yayin harin ƴan bindigan sun yi awon gaba da mutane aƙalla 10 zuwa cikin daji.

Yan bindiga sun kai hari Zamfara.
Yan Bindiga Sun Kai Hari Hedkwatar Karamar Hukuma a Jihar Zamfara Hoto: channelstv
Asali: UGC

An ce maharan sun kutsa kai cikin garin Zurmi da yammacin jiya Talata kuma daga zuwa suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, lamarin da ya tilasta ma jama'a gudun neman tsira.

Kara karanta wannan

Mummunan hatsari ya laƙume rayukan aƙalla mutane 10 a babban titi a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun yi kokarin daƙile harin

Dakarun sojojin rundunar Operation Hadarin Daji sun kai ɗauki garin inda suka yi musayar wuta da ƴan bindigan na tsawon sa'o'i masu yawa.

Wani mazaunin garin, Abubakar Zurmi, ya shaida wa jaridar cewa akalla mutane 10 ciki harda mai jego da sabon jaririn da ta haifa aka yi garkuwa da su a harin.

A kalamansa ya ce:

"Yan ta'adda da yawa suka shigo garin ta kowane ɓangare da misalin ƙarfe 5:30 na yamma, daga zuwa suka buɗe wa mutane wuta."
"A gaskiya sojoji sun yi iya bakin ƙoƙarinsu domin daƙile harin har an ji wa soja ɗaya rauni yayin artabu da ƴan ta'addan."

Abubakar Zurmi ya ci gaba da cewa, "Zuwa yanzun ba a ga mutum 10 ba amma muna da yaƙinin maharan ne suka yi garkuwa da su ciki harda mai jego wacce ta haihu makon jiya."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kutsa kai cikin Abuja, sun tafka mummunar ɓarna tare da kashe jami'in tsaro

Har yanzu da muke haɗa wannan rahoton rundunar ƴan sanda reshen jihar Zamfara ba ta ce komai ba kan wannan sabon harin.

Wani mazaunin yankin, Bello Bashir, ya shaida wa Legit Hausa cewa da yawan mutane ba su yi sallar Magrib da Isha'i a Masallaci ba sanadin harin.

A cewarsa, garin ya zama tamkar babu kowa, wasu sun shiga gida wasu kuma sun bar garin saboda harin ya yi muni.

"Garin Zurmi ya koma kamar ba kowa, mutane sun yi takansu tunda yan ta'adda suka shigo da yamma, muna rokon Allah ya kawo mana ɗauki amma abun ba daɗi," in ji shi.

Haka nan wani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce a gaskiya jami'an tsaro sun yi iya bakin kokarinsu amma ba a ƙaro musu waɗanda zasu taimaka musu wajen daƙile harin ba.

Gobara ta yi ɓarna a sakateriyar Gwale

A wani rahoton na daban Wuta ta babbake ofisoshi 17 a sakateriyar ƙaramar hukumar Gwale ta jihar Kano da safiyar ranar Laraba, 13 ga watan Disamba, 2023.

Hukumar kashe gobara ta jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ta samu kiran gaggawa kuma ta tura motar da ta kai ɗauki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262