Zargin Rashin Lafiya: Gwamna Adeleke Ya Dawo Najeriya, Ya Karyata Masu Jita-Jita
- A yayin da jita-jita ta fara yawaita kan lafiyar Gwamna Adeleke na jihar Osun, wani sabon rahoto ya nuna cewa gwamnan ya dawo Najeriya
- Kwanaki 30 kenan gwamnan ya shafe a kasar Thailand inda ya ce ya je yin hutu, sabanin rade-raden da ake na cewa ya je ayi masa aiki a guiwa
- Dawowar Adeleke ta kawo karshen takaddamar da ake yi a jihar Osun, kan ko gwamnan na da isasshiyar lafiyar da zai ci gaba da gudanar da mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Osun - Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya dawo Najeriya bayan shafe wata daya yana hutu a kasar waje.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa rashin zaman Adeleke a jihar na tsawon kwanaki 30 ya jawo cece-kuce.
Wasu na zargin cewa Adeleke ya fita kasar waje neman maganin ciwon guiwar da yake fama da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me ya kai Gwamna Adeleke Thailand?
Sai dai mai magana da yawun gwamnan, Olawale Rasheed ya ƙaryata jita-jitar, inda ya ce Adeleke ya fita neman masu saka hannun jari ne.
Amma a wata hira da Adeleke a kafar rediyo, ya ce ya je kasar Thailand don ya huta. Ya kuma karyata zargin ya je ayi masa aiki a guiwarsa.
Wani bidiyo da The Nation ta ci karo da shi ya nuna hadiman Adeleke na tarbarsa daga filin jirgin sama cike da farin ciki.
Da aka tuntubi kwamishinan watsa labarai na jihar, Kolapo Alimi, ya tabbatar da cewa Gwamna Adeleke ya dawo kasar a ranar Talata, 12 ga watan Disamba.
Jikin gwamnan Ondo ya tsananta, ya mika mulki ga mataimakinsa
A wani labarin da Legit Hausa ta kawo maku, kun ji cewa rashin lafiyar Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu ya tsananta, inda ya nemi hutu don zuwa Jamus neman magani.
A yayin da zai yi wannan tafiyar, ya mika rikon shugabancin jihar hannun mataimakinsa, Lucky Aiyedetiwa har zuwa lokacin da zai samu lafiya.
Dama dai an dade ana samun rikici siyasa a jihar, tun bayan da 'yan majalisun jihar suka fahimci Akeredolu ba zai iya gudanar da ayyukan ofishinsa ba, lamarin da ya kai ga yunkurin tsige shi.
Asali: Legit.ng