Gobara Ta Babbake Ofisoshi Sama da 15 a Hedkwatar Karamar Hukuma a Kano
- Wuta ta babbake ofisoshi 17 a sakateriyar ƙaramar hukumar Gwale ta jihar Kano da safiyar ranar Laraba, 13 ga watan Disamba, 2023
- Hukumar kashe gobara ta jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ta samu kiran gaggawa kuma ta tura motar da ta kai ɗauki
- Mai magana da yawun hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya ce sun fara bincike domin gano asalin abin da ya haddasa wutar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da cewa wutar da ta kama da safiyar ranar Laraba ta ƙone ofisoshi 17 a sakateriyar karamar hukumar Gwale.
Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar kwana-kwana, Alhaji Saminu Abdullahi, shi ne ya tabbatar da aukuwar lamarin ga hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) a Kano.
Abdullahi ya bayyana cewa gobarar ta tashi a sakatariyar ƙaramar hukumar a awannin farko na safiyar ranar Laraba, 13 ga watan Disamba, 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Punch ta tattaro Abdullahi na cewa:
"Mun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 3:43 na safiya daga wani mai suna Abdullahi Hassan, wanda ya shaida mana cewa wuta ta kama a sakateriyar Gwale."
"Nan take bayan samun wannan bayanan muka tura motar kashe wuta zuwa wurin da misalin ƙarfe 3:46 na safe domin shawo kan lamarin cikin hanzari."
Ɓarnar da wutar ta yi a sakateriyar Gwale
Abdullahi ya ce wurin da aka yi amfani da shi a matsayin ofis mai tsawon ƙafa 300 x 200 da sauransu, wanda a jimulla ya kai ofisoshi 17, ya ƙone gaba ɗaya.
Haka nan kuma ya bayyana cewa wasu motoci uku da aka ajiye a sakatareyar wutar ta shafe su amma ba sosai ba.
Mai magana da yawun hukumar kashe gobarar ya ambaci sunayen motocin da wutar ta taɓa, wanda suka haɗa da 406 Peugeot guda ɗaya, Bas guda ɗaya da motar ujila.
Ya ce a halin yanzu hukumar ta fara bincike domin gano musabbabin abin da ya kawo tashin gobara a sakateriyar Gwale, cewar rahoton Daily Post.
Yan Sanda Sun Gurfanar da Masu Zanga-Zanga a Gaban Kotu
A wani rahoton na daban Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da cewa mutum bakwai da ta cafke kan zanga-zanga, ta gurfanar da su a gaban kotu.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa ya ce an gurfanar da su ne a wata kotun majistare da ke Ungogo.
Asali: Legit.ng