Sun Yi Kadan, Ministar Tinubu Ta Koka Kan Karancin Kudin Ma’aikatarta Don Yakar Talauci

Sun Yi Kadan, Ministar Tinubu Ta Koka Kan Karancin Kudin Ma’aikatarta Don Yakar Talauci

  • Ministar jin kai da walwala ta koka kan yadda aka ba ta kudade kalilan na kasafin ma’aikatarta
  • Dakta Betta Edu ta yi korafin cewa kudaden kwata-kwata ba za su ishe su yakar talauci ba a kasar
  • Ministar ta bayyana haka ne a yau Talata 12 ga watan Disamba yayin ganawa da kwamitin Majalisar Dattawa ta bangaren jin kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Ministar jin kai da walwalar jama’a, Dakta Betta Edu ta yi korafin karancin kudade a ma’aikatarta.

Edu ta bayyana cewa kudaden kasafi na ma’aikatarta ba zaza su iya yakar talauci ba da ta ke kokarin yi, cewar TheCable.

Kudin da aka ware mana ya yi kadan mu yaki talauci, Ministar Tinubu ta koka
Betta Edu ta yi korafi kan karancin kudi da aka ware a ma'aikatarta. Hoto: Bola Tinubu, Betta Edu.
Asali: Getty Images

Mene Ministar ta ke korafi a kai?

Kara karanta wannan

Yan Najeriya na fama da matsin tattalin arziki yayin da gwamnatin Tinubu ke sharholiya - Rahoto

Ministar ta bayyana haka ne a yau Talata 12 ga watan Disamba yayin ganawa da kwamitin Majalisar Dattawa ta bangaren jin kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Betta ta ce an bai wa ma’aikatarta naira biliyan 532 wanda ya karu da kashi 28 idan aka kwatanta da na shekarar 2023, cewar Daily Times.

Ta tabbatar da cewa karin kaso 28 babu abin da zai yi idan aka kwatanta da hauhawan farashin kayayyaki a kasa a yanzu.

Ta ce:

“A cikin shekarar 2022 da 2023 an samu raguwar kaso 71 daga cikin dari saboda a 2022 ya kai biliyan 3.7 yayin da a 2023 kuma biliyan 1.32.
“Ha ila yau, karuwar da aka samu a yanzu babu yadda za a yi ya iya kawo karshen talauci da mu ke fatan yaka.”

Wace bukata Ministar ta nema?

Dakta Edu ta roki shugaban kwamitin da mambobinsa don hubbasa wurin ganin an yaki talauci a kasar.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Yan sanda sun kama matashi yana lalata da zakara a jihar Adamawa

Ta ce abin da su ka sani da ita da wadanda su ke aiki karkashinta shi ne Shugaba Tinubu ya himmatu wurin dakile talauci a kasar.

Ta kara da cewa:

“Kamar yadda kuka sani, Tinubu ya amince da kirkirar asusun yaki da talauci a kasar.
“Wannan asusu za ta na samun kaso 30 daga Gwamnatin Tarayya da kuma sauran masu tallafawa na kasashen ketare.”

NLC ta gargadi Tinubu kan biyan dubu 35

A wani labarin, Kungiyar NLC ta gargadi Shugaba Tinubu kan dakatar da biyan kudaden rage tallafi na naira dubu 35.

Wannan na zuwa ne bayan an biya kudaden na wata daya kacal a watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.