Watakila ASUU Ta Tafi Yajin Aiki a 2024 Saboda Tinubu Ya Saba Alkawarin da Ya Dauka
- Emmanuel Oshodeke ya ce 7% kacal gwamnatin tarayya ta ware za a kashewa bangaren ilmi a Najeriya a 2024
- Shugaban kungiyar ta ASUU ya koka kan yadda Bola Tinubu ya saba alkawarin da ya dauka a yayin yakin zabe
- Farfesa Oshodeke yake cewa an yi alkawarin warewa ilmi 15%, amma ba ayi haka a cikin kasafin kudin badi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abuja - Ba abin mamaki ba ne a shekara mai zuwa ta 2024, malaman jami’o’in gwamnati su shiga yajin-aikin da aka saba yi a kasar.
Da Punch ta yi hira da shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Emmanuel Oshodeke, ya bayyana cewa ana cigaba da yin watsi da sha’anin ilmi.
ASUU: "Babu abin da ya canza zani"
Farfesa Emmanuel Oshodeke ya ce a lokacin yakin neman zabe, Bola Ahmed Tinubu ya ce zai warewa ilmi 15% a cikin kundin kasafin kudi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan ya karbi mulki sai ga shi Mai girma Bola Ahmed Tinubu bai cika alkawarin da ya dauka ba, kungiyar ASUU tace ana nan a gidan jiya.
Farfesan ya ce kungiyar malaman jami’an ta yi tir da jin N2.18tr kacal aka ware domin harkar ilmi a kasafin kudin shekara mai zuwa.
ASUU ta ce ba a cika sharudan UNESCO ba
UNESCO ta bada shawarar ayi wa ilmi tanadin 26%, amma abin da gwamnatin tarayya za ta kashe 7.9% ne rak na kasafin kudin kasar.
Oshodeke ya ba Bola Tinubu shawarar ya zauna da jami’an gwamnatin tarayya domin ganin an kara kason zuwa 15% ko sama da haka.
"Da wannan 7%, babu abin da zai canza zani a bangaren ilmi, kamar yadda yake ne a lokacin Muhammadu Buhari.
Lokacin yakin neman zaben shi, Tinubu ya yi alkawarin kasa kason ilmi, amma bai yi ba."
- Farfesa Emmanuel Oshodeke
ASUU za ta tafi yajin-aiki a shekarar 2024?
Daily Post ta rahoto shugaban na ASUU ya ce idan ba ayi komai ba, zuwa shekara mai zuwa zai hada-kan kungiyar domin a dauki mataki.
ASUU tana so a kara albashin malamai, kara shekarun ritaya, bada damar yaye masu PhD, kuma a bambanta su da sauran ma’aikatan gwamnati.
Tinubu zai hana ASUU yajin-aiki
Babu maganar yajin-aikin kungiyar ASUU a jami’o’i idan Bola Ahmed Tinubu ya na kan karagar mulki kamar yadda aka samu labari a baya.
Tinubu ya ce babu dalibin da zai bar makaranta a dalilin gaza biyan kudi a mulkinsa, ya fadi haka ne a wajen taron yaye daliban jami’ar FUTO.
Asali: Legit.ng