Yanzun Nan: Gobara Ta Tashi a Ofishin Gwamnan Jihar Borno
- Gobara ta tashi a ofishin Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a ranar Talata, 12 ga watan Disamba
- An rahoto cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 12: 29 na ra lokacin gwamnan na daya ofishinsa a sakatariyar Musa Usman
- Yanzu haka yan kwana-kwana sun dukufa aikin tabbatar da kashe wutan yayin da yan sanda suka hana motoci, mutane da manema labarai shiga gidan gwamnatin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Birno - Rahotanni da ke zuwa sun kawo cewa gobara ta tashi a ofishin gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum a safiyar yau Talata, 12 ga watan Disamba.
Kamar yadda Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X ( wanda aka fi sani da Twitter a baya) ya ce zuwa yanzu ba a tabbatar da irin barnar da gobarar da ta kama ainahn ofishin gwamnan ta yi ba.
Yan kwana-kwana sun kai dauki
An tattaro cewa gwamnan na a daya ofishinsa da ke sakatariyar Musa Usman lokacin da lamarin ya afku da misalin karfe 12:29 na rana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rahoto cewa an gano motocin hukumar kwana-kwana suna fita daga gidan gwamnati a kokarinsu na kashe gobarar.
Rundunar yan sanda sun hana motoci, ma’aikata da manema labarai shiga gidan gwamnatin tun daga babban kofar shiga.
Motar mai ta fashe a Kaduna
A wani labari na daban, mun ji cewa wata babbar motar dakon mai ɗauke da man dizel ta fashe kuma ta yi filla-filla a yankin Ojota da ke jihar Legas ranar Litinin, 4 ga watan Disamba, 2023
Hukumar kula da zirga-zirgan ababen hawa ta jihar Legas, (LASTMA), ce ta tabbatar da aukuwar ibtila'in a shafinta na manhajar X wadda aka fi sani da Tuwita.
Hukumar ta kuma bayyana cewa tuni ta tura jami'anta zuwa wurin domin kai agajin da ya kamata da kuma shawo kan lamarin a kan lokaci.
Gobara ta lakume dukiya a Jigawa
A wani labarin kuma, mun ji cewa shaguna da kayayyaki masu daraja da kudinsa ya kai miliyoyi sun lalace a Bakin Kasuwa da ke Karamar Hukumar Hadejia na jihar Jigawa a ranar Juma'a.
Adamu Shehu, mai magana da yawun Hukumar Tsaro na NSCDC na jihar ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Asabar.
Asali: Legit.ng