'Yan Bindiga Sun Kutsa Kai Cikin Abuja, Sun Tafka Mummunar Ɓarna Tare da Kashe Jami'i

'Yan Bindiga Sun Kutsa Kai Cikin Abuja, Sun Tafka Mummunar Ɓarna Tare da Kashe Jami'i

  • Ƴan bindiga sun sake kai hari wani ƙauye a babban birnin Abuja, sun kashe jami'in tsaro tare da sace wasu mutum 12
  • Mazauna yankin sun ce yan banga sun yi kokarin daƙile harin amma yan bindigan suka ci ƙarfinsu da makamai
  • Har kawo yanzu ba su tuntubi dangin waɗanda suka sace ba, amma harin ba shi ne na farko a kauyen Gbaupe ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hare-haren ta'addanci na ƙara ƙaruwa a babban birnin tarayya Abuja yayin da ƴan bindiga suka kai sabon hari Gbaupe, kauyen da ke bayan rukunin gidajen Lugbe.

Yan bindiga sun shiga Abuja.
Mutum Daya Ya Musu Yayin da Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa da Mutane 12 a Abuja Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa a harin da ƴan ta'addan suka kai ƙauyen wanda ke gefen titin filin jirgi a Abuja, sun sace bayin Allah 12 ciki harda 'yar shekara 13.

Kara karanta wannan

Mako ɗaya bayan jefa bam a Kaduna, 'yan bindiga sun ƙara yin mummunar ɓarna kan bayin Allah

Wani mazaunin ƙauyen ya shaida wa jaridar cewa maharan sun kai sabon harin ne ranar Lahadi, 10 ga watan Disamba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar mutumin, biyu daga cikin mutanen da maharan suka yi garkuwa da su sun gudo yayin da ƴan bindigan ke shirin kutsawa da su ta cikin daji.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun tafi da wani mutum ɗaya daga cikin mutanen da suka sace, babu riga da takalmi a jikinsa.

Duk da cewa ba wannan ne karon farko da mahara suka kai wa Gbaupe hari ba, amma ba a taba samun harin garkuwa mai girman na ranar Lahadin nan ba a ƙauyen.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Dakarun rundunar ƴan banga sun kai ɗauki tare da fafatawa da masu garkuwan amma aka ci ƙarfinsu sabida maharan su fi su manyan makamai, suka kashe jami'i ɗaya.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai sabon farmaki a fada, sun yi awon gaba da babban basarake

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton yau Talata da safe, masu garkuwa da mutanen ba su tuntubi dangogin waɗanda suka yi garkuwa da su ba, Daily Trust ta tattaro.

Masu garkuwa da mutane sun shafe sama da shekaru uku suna kai hare-hare yankunan Gbau, Kuje, Gauge, Pegi, Abaji, Keti, da kuma Kwali duk a Abuja ba tare da fuskantar turjiya daga jami'an tsaro ba.

Yan Bindiga Sun Kara Yin Mummunar Ɓarna Kan Bayin Allah a Kaduna

A wani rahoton na daban Ƴan bindiga sun yi garkuwa da kauyawa akalla 30 a wani sabon hari da suka kai Unguwar Liman da ke ƙaramar hukumar Igabi a Kaduna.

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun tafi mutane ciki harda mata da ƙananan yara da jariran da ake shayarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262