“Ina Kashewa Motata N1.4m Duk Wata, N324k Kan Inshora”: Matashi da ke Tuka Tsadaddiyar Mota
- Wani matashi da ya mallaki tsadaddiyar motar Benz C Class Coupe ya bayyana cewa yana kashe makudan kudade duk wata
- Baya ga kashe £160 kan man fetur, yana biyan abubuwa kamar su inshorar titi da mota da ke jan kaso mai yawa daga albashinsa
- Yan TikTok da dama da suka ga bidiyon sun bayyana cewa da zai fi kyau idan mutumin ya zuba jari a wasu wuraren
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wani matashi da ke aiki mai kyau a Turai ya bayyana abun da yake kashewa wajen kula da tsadaddiyar motarsa wanda ya hada da inshora.
Baya ga £3,000 (N4,428,375) da ya fara ajiyewa na motar Mercedes Benz C Class Coupe, yana biyan £300 (N442,837) duk wata da £220 (N324,747.5) na inshora. Harajin hanya £50 (N73,806.25) a wata.
Kudin da ake kashewa kan insorar mota a Birtaniya
Shi (@cksgallery) ya kashe £160 (N236,180) kan man fetur. Mutumin ya bayyana cewa baya ga uwar kudin, ya kashe kudi kan abubuwa kamar birki da tayoyinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matashin ya bayyana cewa ya zama dole ya ajiye tsakanin £900 (N1,328,512.5) da £950 (1,420,318) a wata don kula da motarsa. Ya shawarci matasa a kan kada su yi gaggawan shiga rayuwar tuka mota domin yana da matukar tsada.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
Lenasx ta ce:
"Kuma duk da an burge mutane ne."
W.G ya ce:
"Bai kamata kudin harajin hanyarka ya yi yawa ba."
kurt6221 ya ce:
"Diesel amma ka ce 180 kan man fetur, kuskure."
S ya ce:
"Yana da matukar sauki siyan mota amma idan aka zo maganar kula da itya aljihunka zai sha kashi."
Sunny b ya ce:
"Na mallaki motar c class coupe kuma harajin hanyata £20ne a shakara dan uwa."
TKP ya ce:
"Dan uwa nima ta kasance da ni, ina son motar, duba ga lissafin kana kashe makudan kudade kan motar nan. zan siyar na zuba kudin a wani mai arha sannan in tara.
Farfesa ya kama aikin walda
A wani labari na daban, wani farfesan jami'ar Najeriya, Kabir Ahmed Abu-Bilal, ya dauka hankali bayan ta bayyana cewa aikin walda yake yi.
Farfesan mazaunin Kaduna ya ce abun da yake samu daga shagonsa a wata ya ninka albashinsa na wata a matsayin farfesa, yana mai cewa wannan na daya daga cikin dadin da ke tattare da aikin hannu.
Asali: Legit.ng