Mako Ɗaya Bayan Jefa Bam a Kaduna, Yan Bindiga Sun Kara Yin Mummunar Ɓarna Kan Bayin Allah

Mako Ɗaya Bayan Jefa Bam a Kaduna, Yan Bindiga Sun Kara Yin Mummunar Ɓarna Kan Bayin Allah

  • Ƴan bindiga sun yi garkuwa da kauyawa akalla 30 a wani sabon hari da suka kai Unguwar Liman da ke ƙaramar hukumar Igabi a Kaduna
  • Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun tafi mutane ciki harda mata da ƙananan yara da jariran da ake shayarwa
  • An yi ƙoƙarin samun tabbacin abin da ya faru daga bakin kakakin yan sandan jihar amma hakan bai cimma nasara ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Wasu miyagun 'yan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla mutane 30 a kauyen Unguwar Liman da ke yankin Gwada a ƙaramar hukumar Igabi, jihar Kaduna.

Yan bindiga sun kai kazamin hari a Kaduna.
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mutane 30 a Kauyen Jihar Kaduna Hoto: dailytrust
Asali: Twitter

Mazauna ƙauyen sun bayyana cewa waɗanda maharan suka sace sun haɗa da mata da ƙananan yara ciki har da jariran da ba su kai shekara biyu da haihuwa ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kutsa kai cikin Abuja, sun tafka mummunar ɓarna tare da kashe jami'in tsaro

Kamar yadda Daily Trust ta tattaro, ƴan bindigan sun kai farmaki garin da misalin ƙarfe 11:00 na daren ranar Lahadi kuma daga zuwa suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin yankin kuma shugaban al'umma, Malam Jafar Anaba, ya shaida wa ƴan jarida ranar Litinin cewa ɗan uwansa na jini da wasu danginsa na cikin waɗanda aka sace.

Yan bindigan sun nemi kuɗin fansa?

Ya bayyana cewa har kawo yanzu ƴan bindigan ba su tuntuɓi iyalan mutanen da ke hannunsu domin neman kuɗin fansa ba, Channels tv ta ruwaito.

A kalamansa ya ce:

"Sun shiga ƙauyen kuma suka kwashi mutane kusan 30, ɗan uwana na jini da wasu mambobin dangin gidanmu na cikin waɗanda 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a harin ranar Lahadi da daddare."

Ya ce mazauna yankin sun yi kokarin neman agaji a daren da aka kai harin da kuma washegari, amma babu hanyar sadarwa a lokacin saboda sabis ya ɗauke.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai sabon farmaki a fada, sun yi awon gaba da babban basarake

Duk wani yunƙuri da aka yi domin jin ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, bai kai ga nasara ba.

Lamabar wayansa ta ƙi shiga kuma bai amsa sakonnin kar ta kwana da aka tura masa kai tsaye ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Wannan na zuwa ne mako ɗaya daidai bayan jirgin sojojin ƙasa ya yi kuskuren jefa bam a Tundun Biri, ƙauyen da ke ƙaramar hukumar Igabi, inda mutane sama da 100 suka rasu.

Yan Bindiga Sun Tarwatsa Mutanen Gari Guda a Kaduna

A wani rahoton na daban Miyagun 'yan bindiga sun kai mummunan harin kauyen Kidandan da ke yankin ƙaramar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

Mazauna garin maza da mata da ƙananan yara sun tattara sun bar garin bayan harin wanda yan bindigan suka kashe mutane da yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262