Kungiyar Arewa Ta Gano Dalilin Tinubu Na Janye Sunan El-Rufai, Kwankwaso a Nadin Ministoci
- Wata kungiyar matasan Arewa ta yi ikirarin cewa akwai shirin da ake yi na gurgunta 'yan siyasar Arewa don cimma wata manufa a zaben 2027
- Kungiyar mai suna CNYMI, ta kuma lissafa wasu 'yan siyasa daga yankin Arewa da gwamnatin Tinubu ta kunyata da suka hada da Nasir El-Rufai
- Sai dai kungiyar ta yi gargadin cewa ba za ta lumunci duk wani shiri da zai kawo koma baya ko cin fuska ga al'ummar Arewa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Kaduna - Kungiyar hadakar kungiyoyin matasan Arewa (CNYMI) ta yi zargin cewa akwai wani shiri da aka yi na gurgunta manyan 'yan siyasar Arewa gabanin zaben 2027.
Kungiyar ta yi kira ga fannin shari'a, jami'an tsaro da hukumar INEC da su rike alkawarin da suka dauka na yin aiki bisa gaskiya, inda suka ce ba za su lamunci nakasa Arewa ba.
Kungiyar ta kuma gargadi 'yan siyasa da su guji sa hannu wajen a abubuwan da ka iya kawo koma baya ga al'ummar yankin Arewa, rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanne 'yan siysa ne ake son gurguntawa Arewa?
Shugaban kungiyar, Hamza Bala Lawal, wanda ya samu wakilcin sakataren kungiyar, Ibrahim Muhammad Inuwa shi ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a Kaduna.
Ya ce:
"Shugaban kungiyar ya yi zargin cewa akwai wani yunkuri da ake yi na nakasa 'yan siyasar Arewa don cimma wata manufa a zaben 2027."
Legit ta ruwaito Lawal na lissafo wasu 'yan siyasar Arewa da Shugaba Tinubu ya kunyata a idon duniya da suka hada da, Malam Nasir El-Rufai da Sanata Abdulazeez Yari da Rabiu Kwankwaso.
Lawal ya kara da cewa:
"Wani dan Arewa da shi ma aka kunyatar tun bayan hawan wannan gwamnatin shi ne Sanata Ali Ndume, wanda ya cancanci zama shugaban majalisar dattawa amma aka kitsa tuggun hana shi."
Jam'iyyar APC ta kori shugaban karamar hukuma a jihar Niger
A wani labarin, kun karanta cewa jam'iyyar APC ta dakatar da wani Gambo Ibrahim, shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Suleja, jihar Niger.
Jam'iyyar ta dauki wannan matakin ne bayan kwamitin gudanarwar jam'iyyar ya sami Ibrahim da aikata laifukan da suka shafi karbar rashawa, Legit Hausa ta ruwaito.
Asali: Legit.ng