An Shiga Jimami Yayin da Shahararriyar Ma’aikaciyar NTA, Aisha Bello Ta Riga Mu Gidan Gaskiya
- Allah ya karbi rayuwar shahararriyar ma’aikaciyar gidan talabijin na NTA, Aisha Bello a jiya Lahadi
- An samu rahoton rasuwar tata a a jiya Lahadi 10 ga watan Disamba inda aka sanar da jana’izarta karfe 1 na rana a masallacin Abuja
- Kafin rasuwarta, Aisha ita ce babbar manaja a bangaren shirin Majalisa a NTA wacce ta shafe shekaru 30 ta na labaru
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – An shiga jimami bayan rasuwar kwararriyar ma’aikaciyar gidan talabijin na NTA, Aisha Bello.
Mutuwar marigayiyar ya girgiza intanet inda ‘yan Najeriya su ka nuna kaduwarsu kan wannan babban rashi.
Yaushe marigayiyar ta rasu?
An samu rahoton rasuwar marigayiyar a jiya Lahadi 10 ga watan Disamba sai dai ba a bayyana silar mutuwar tata ba.
Innalillahi: Babban limamin masallacin Tede kuma shugaban majalisar malamai ya riga mu gidan gaskiya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit ta tattaro cewa za a yi sallar jana’izar marigayiyar yau Litinin 11 ga watan Disamba a babban masallacin Abuja da misalin karfe 1 na rana.
Kafin rasuwarta, Aisha ta rike mukamin babbar manaja a bangaren shirin Majalisa a NTA wacce ta shafe shekaru 30 a matsayin mai labaru tun shekarun 1990.
Ta kuma yi aiki tare da kwararren ma’aikacin NTA, Cyril Stober wanda ya yi ritaya a shekarar 2019.
Marigayiyar ta yi rataya a matsayin babbar manajar sashin shirin Majalisa a NTA a watan Mayun 2022.
Wane martani iyalan marigayiyar su ka yi?
Iyalan marigayiyar sun fitar da sanarwa kan rasuwar inda su ka bayyana ta a matsayin mace mai kirki.
Sanarwar ta ce:
"Innalillahi wa inna ilahir rajiun, Allah ya gafarta wa mamarmu Hajiya Aisha Bello Mustapha.
"Mama, tabbas ke mutumiyar kirki ce,mu na fatan kina cikin rahama, za a yi sallar jana'izarta a yau Litinin 11 ga watan Disamba da misalin karfe 1 na rana a masallacin Abuja."
Babban limamin Tede ya riga mu gidan gaskiya a Oyo
A wani labarin, an shiga jimami bayan rasuwar babban limamin masallacin Tede, Alhaji Ahmed Tijani Adedigba a jihar Oyo.
Kafin rasuwar marigayin, shi ne shugaban majalisar malaman Oke Ogun a karamar hukumar Atisbo da ke jihar.
Gwamna Seyi Makinde ya nuna alhininsa kan wannan babban rashi inda ya ce al'ummar Musulmai za su yi keyar mamacin saboda irin gudunmawar da ya bayar.
Asali: Legit.ng