Gwamna Bala Mohammed Ya Yi Muhimman Nade-Nade a Gwamnatinsa

Gwamna Bala Mohammed Ya Yi Muhimman Nade-Nade a Gwamnatinsa

  • Gwamnan Jihar Bauchi ya yi naɗin sabbin manyan mataimaka na musamman waɗanda za su yi aiki a gwamnatinsa
  • Gwamna Bala Mohammed ya amince da naɗin manyan mataimaka na musamman da mataimaka na musamman 28
  • Mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai ne ya tabbatar da naɗe-naɗen a cikin wata sanarwa da ya fitar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya amince da naɗin manyan mataimaka na musamman guda 28.

Naɗin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar a ranar Lahadi, 10 ga watan Disamba, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Kwamishina ya faɗi gaskiya, ya tona asirin jiga-jigan gwamnati da ke jabun sa hannun gwamnan APC

Gwamna Bala Mohammed ya yi nade-nade
Gwamna Bala Mohammed ya yi sabbin nade-nade Hoto: Senator Bala Mohammed
Asali: Twitter

Sanarwar an yi mata taken, ‘Naɗin manyan mataimaka na musamman (SSA) da mataimaka na musamman ga gwamna.'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce matakin da gwamnan ya ɗauka wani yunkuri ne na inganta shugabanci nagari, da tafiya da kowa, rahoton Platinum Times ya tabbatar.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Mutanen da aka zaba sun nuna ƙwazo na ƙwarai ga cigaban jihar Bauchi, tare da samar da ɗabi’u da hangen nesa na gwamna."
"Ana sa ran sabbin manyan mataimaka na musamman da mataimaka na musamman za su kawo dimbin gogewa da ƙwarewa wajen aiwatar da manufofi da tsare-tsare na gwamnati da suka dace da bukatun al’ummar jihar Bauchi."

Su wanene aka naɗa muƙaman?

A cewarsa manyan mataimaka na musamman (SSA) da aka naɗa sun haɗa da:

  • Abubakar Yari - Ayyuka na musamman
  • Musa Sulaiman - Ofishin Gwamna
  • Al-Ameen Zirami - Harkokin Addini
  • CP Hamisu Makama (mai ritaya) - Harkokin ƴan sanda
  • El-Harun Dambam - Harkokin sadarwar zamani
  • Khalid Barau - Samar da ayyukan yi
  • Garba Alkaleri - Ayyuka na musamman
  • Eric Anyamene - Dabaru da ayyuka na musamman
  • Hassan Grema - Harkokin Sadarwa
  • Adamu Barde - ACRESAL
  • Bala Saleh - Matasa
  • Lawal Muazu - Sabuwar kafar sadarwa
  • Aminu Kobi - Gudanar da zirga-zirga
  • Magaji Zakka - Harkokin addinin Kirista
  • Hafiz Mai-Auduga - Kasuwanci da masu Sana'o'i
  • Habiba Alkaleri - Ofishin uwargidan gwamna
  • Sulaiman Ahmed - Tsare-tsare
  • Sani Mohammed - Tsaro
  • Nasiru Yahuza - Ƙanana da matsakaitan masana’antu
  • Yahaya Baba - Siyasa

Kara karanta wannan

Atiku da Ɗangote sun lale Naira biliyan uku sun baiwa ɗan takarar gwamna a arewa? Gaskiya ta yi halinta

Jerin waɗanda aka naɗa mataimaka na musamman

Bugu da ƙari, ya ce mataimaka na musamman su ne:

  • Ishaya Dangana - Siyasa
  • Bukata Ishaya - Ofishin Gwamna
  • Kabir Musa - Ayyukan cikin gida
  • Mohammed Aljyu - Ayyukan cikin gida
  • Auwal Abdullahi - Tsare-tsare na ofishin uwargidan gwamna
  • Lawal Toro - Hoto
  • Musa Zango - Tiransifomomi
  • Joshua Yewuri - Cigaban al'umma

Ya ce naɗin na su ya fara aiki nan take.

Gwamna Abba Ya Yi Sabbin Nade-Nade

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi sabbin naɗe-naɗe da sauya wa wasu wuraren aiki a gwamnatinsa.

Daga cikin waɗanda aka sauya wa wurin aiki har da Sanusi Dawakin Tofa wanda ya samu ƙarin matsayi daga sakataren yaɗa labarai zuwa Darekta Janar na harkar yaɗa labarai da hulɗa da jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng