Abun Bakin Ciki Yayin da Wani Mutum Ya Kashe da Birne Mahaifiyarsa da Kanwarsa a Karamin Rami
- Jami'an yan sanda sun kama wani matashi, Somadina Orji, kan kisan mahaifiyarsa da kanwarsa a jihar Enugu
- Somadina ya binne su a cikin kananan rami a bhayan gidansu da ke Umuagu Inyi, karamar hukumar Oji River da ke jihar
- An gani mummunan al'amarin ne lokacin da kaninsa ya koka bayan ya dawo bai ga mahaifiyar ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Umuagu Inyi, jihar Enugu - Yan sanda sun kama Somadina Orji mai shekaru 25 kan zargin kashe mahaifiyarsa, Misis Charity, da kanwarsa Miss Ukamaka, sannan ya binne su a karamin rami a bayan gidansu da ke jihar Enugu.
Mummunan al'amarin ya afku ne a ranar Litinin, 4 ga watan Disamba, 2023, a Umuagu Inyi, karamar hukumar Oji River ta jihar, rahoton Punch.
An tattaro cewa Somadina ya fito ne daga Igboariam a jihar Anambra yayin da mahaifiyarsa ta fito daga Inyi a jihar Enugu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani jigon garin, Barista Ben Obi, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai ya ce matsalar ta fara ne yan makonni da suka gabata lokacin da mai laifin ya so kashe kaninsa, rahoton The Nation.
Mahaifiyar ta kai rahoton lamarin gaban manyan gari sannan ta nemi su kore shi daga gidan.
A cewar Obi, matashin ya kashe ta sannan ya binne ta a wani karamin rabi a bayan gidansu bayan ta dawo daga ziyarar ta'aziyya a Akpugoeze.
Ya ce, kanin ya koka ne bayan ya dawo bai ga mahaifiyar ba.
"Lokacin da mutanen kauyen suka taru a harabar gidan da ake yi masa tambayoyi, Somadina ya amsa cewa ya kashe mahaifiyar."
Ya kuma yi ikirarin cewa ya kashe kanwar ne yan makonnin da suka gabata.
Jigon garin ya kara da cewa an gayyaci yan sanda tare da tono gawar uwar da yar uwar tasa, sannan aka ajiye su a dakin ajiyar gawa.
Yan sanda za su fara kama masu kudi
A wani labarin, rundunar yan sandan jihar Delta ta yi kira ga binciken mutanen da ba za su iya yin bayani mai gamsarwa kan tushen arziki da inda suke samun kudaden shigarsu ba, tana mai cewa ya kamata a bincike su tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Kakakin rundunar, Bright Edafe, ne ya yi wannan kira yayin da yake kira ga yan Najeriya da su dauki binciken arzikin da ba a gamsu da su ba a matsayin matakin kare al’umma daga barazanar garkuwa da mutane, kashe-kashe don kudin asiri, da zamba.
Asali: Legit.ng