Gwamnatin Tinubu Ta Ware Wadanda Za Ta Ci Gaba da Tafiya da Su a Shirin N-Power, Da Kuma Dalilai
- Shirin N-Power na daya daga cikin shirye-shiryen gwamnatin APC na kasa baki daya da nufin tallafawa nau’in matasa daban-daban
- Majiyar Legit ta ruwaito cewa, shirin da aka kafa a 2016, ya rabu kashi biyu; tsarin masu karatu da kuma na wadanda ake ba horon makamar aiki
- Yayin da aka sallami shirin wadanda suka yi karatu a karkashin N-Teach, N-Agro, da N-Health, ba a dakatar da shirin N-Power karkashin N-Creative ba
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
FCT, Abuja – Shirin gwamnatin tarayya na N-Power ya ce shirinsa na wadanda ba su wadanda basu yi karatu mai zurfi ba har yanzu yana nan ba a gama shi ba.
Gudanarwar shirin ta shafinsa na Twitter ya bayyana matsayar gwamnati da ma’aikatar jin kai game da shirin da aka dade ana yi.
A cewarsu:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Shirin mu na wadanda marasa digiri ne na aiki har yanzu.”
Menene shirin N-Power?
Legit ta ruwaito cewa N-Power wani shiri ne na samar da ayyukan yi da kuma karfafawa shirin zuba jari na gwamnatin tarayyar Najeriya.
An tsara shirin ne don taimakawa matasan Najeriya su samu da habaka kwarewar rayuwa don zama masu samar da mafita a cikin al'ummominsu da kuma zama kwararru a kasuwar aiki a duniya.
Wani hali ‘yan N-Creative ke ciki?
Sanarwar ta N-Power ta ce:
“Tsagin wadanda basu yi zurfin karatu ba yana nan daram, a lura cewa duk shirye-shiryen sun tsaya cik a yanzu sakamakon binciken da mai girma Minista ke yi.
"Muna tabbatar wa duk wadanda suka cancanta cewa za mu warware dukkan wasu matsaloli da zarar mun kammala bincike."
Yadda kasar waje ke neman ma’aikata ido rufe
A wani labarin na daban, sakamakon raguwar ma'aikata a fannin fasaha, Singapore tana gayyatar kwararru 260,000 don cike gibin ma’aikinta.
Yayin da take fuskantar karancin ma’aikata, kasar na bukatar habaka karfin ma'aikata don cike gibi a fannin IT da zubin na’ura, banki, da aikin injiniya.
Wani rahoton fasaha ya nuna cewa, wannan wani bangare ne na kokarin da take yi na magance illar ficewar ma’aikatan kasashen waje da annoba ta haifar da ya kai ga rasa ma’aikata sama da 194,000.
Asali: Legit.ng