Shettima Ya Gwangwaje Daliban Koyon Aikin Jinya Na Al-Hikmah da N5m Kan Gabatar Masa da Hotonsa

Shettima Ya Gwangwaje Daliban Koyon Aikin Jinya Na Al-Hikmah da N5m Kan Gabatar Masa da Hotonsa

  • Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya ba daliban koyon aikin jinya na jami’ar Al-Hikmah kyautar naira miliyan 5
  • An gano Shettima a bidiyo yana umurtan daliban da su je su karbi naira miliyan 5 daga hannun shugabansu
  • Da farko tsohon gwamnan na jihar Borno ya bai wa dalibai mata da basu da gata tallafin karatu na naira miliyan 25

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Ilorin, jihar Kwara - Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya bayar da kyautar kudi naira miliyan 5 ga daliban koyon aikin jinya na jami’ar Al-Hikmah da ke Ilorin, jihar Kwara.

Shettima ya ba daliban koyon aikin jinyan kyautar kudin bayan sun gabatar masa da wani hotonsa.

Kara karanta wannan

"Sha'awa ce": Yadda farfesan jami'ar ABU ya kama aikin walda a matsayin sana'a

Shettima ya ba dalibai kyautar naira milyan 5
Shettima Ya Gwangwaje Daliban Karatun Jinya Na Al-Hikmah da Kyautar N5m Kan Gabatar Masa da Hotonsa Hoto: Senator Kashim Shettima
Asali: Facebook

Wani malamin jami’ar mai suna Sanusi Lafiagi, ne ya wallafa bidiyon a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) @sirnucy.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shettima ya kasance a jami’ar ne don gabatar da jawabi a taron yaye dalibai karo na 13 kan matakin ilimi da horar da al’ummar kasar yadda za su yi amfani da damar ci gaban kimiyya a kowani bangare.

A wani bidiyo da lakcaran na Al-Hikmah ya kuma wallafa, Shettima ya sanar da bayar da tallafin karatu na naira miliyan 25 ga hazikan dalibai mata na jami’ar wadanda ba su da hanyar biyan kudin makarantasu.

Shettima ya magantu kan yankunan kasar

A wani labarin kuma, mun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya tabbatar da cewa kowane yanki na ƙasar nan zai amfana da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Atiku da Ɗangote sun lale Naira biliyan uku sun baiwa ɗan takarar gwamna a arewa? Gaskiya ta yi halinta

Ya bayyana cewa tabbatar da cewa babu wani yanki da aka bari a baya a ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen kawo cigaba, shi ne hanya mafita wacce zaman lafiya da haɗin kai zai haɓɓaka, cewar rahoton Leadership.

A cewar wata sanarwa daga mai magana da yawun bakinsa, Stanley Nwocha, Shettima ya bayar da tabbacin ne lokacin da ya karɓi baƙuncin Basaraken Mangu, Mishkahan Mwaghavul, Mai martaba John Hirse wanda ya jagoranci wata tawaga da ta kai masa ziyara a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel