Kashim Shettima Ya Bayyana Yankin da Zai Amfana da Mulkin Shugaba Tinubu

Kashim Shettima Ya Bayyana Yankin da Zai Amfana da Mulkin Shugaba Tinubu

  • Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya tabbatar da cewa babu yankin da ba zai amfana ba a mulkin Tinubu
  • Mataimakin shugaban ƙasan ya tabbatar da hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin basakaren Mangu a ofis ɗinsa
  • Kashim ya bayar da tabbacin cewa Shugaba Tinubu na bakin ƙoƙarinsa domin kawo ƙarshen rikicin Mangu da sauran sassan ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya tabbatar da cewa kowane yanki na ƙasar nan zai amfana da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Ya bayyana cewa tabbatar da cewa babu wani yanki da aka bari a baya a ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen kawo cigaba, shi ne hanya mafita wacce zaman lafiya da haɗin kai zai haɓɓaka, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya bayyana wata muhimmiyar nasara da ya samu a gwamnatinsa

Kashim Shettima ya yi magana kan gwamnatin Tinubu
Kashim Shettima ya ce kowane yanki zai amfana da mulkin Tinubu Hoto: Kashim Shettima
Asali: Twitter

A cewar wata sanarwa daga mai magana da yawun bakinsa, Stanley Nwocha, Shettima ya bayar da tabbacin ne lokacin da ya karɓi baƙuncin Basaraken Mangu, Mishkahan Mwaghavul, Mai martaba John Hirse wanda ya jagoranci wata tawaga da ta kai masa ziyara a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane ƙoƙari Shugaba Tinubu yake yi?

Mataimakin shugaban ƙasar ya tabbatar wa tawagar cewa za a samu zaman lafiya a garin Mangu cikin kankanin lokaci, inda ya ce shugaba Tinubu na bakin ƙoƙari kan lamarin don haka babu makawa a dawo da zaman lafiya a duk sassan ƙasar nan da ke fama da rikici.

A kalamansa:

"Rikicin jihar Plateau ba shi da alaƙa da addini. Shi ne kawai mu fahimci kanmu kuma mu zauna tare cikin lumana da juna. Jihar Plateau ƙasa ce mai albarka da musulmi da kirista. Abin da ya haɗa mu tare ya wuce abin da ya raba mu."

Kara karanta wannan

An gaya wa kotun koli wanda za ta ayyana ya yi nasara tsakanin Gwamna Dauda Lawal da Matawalle

"Wannan gwamnatin za ta yi amfani da duk wani abu don magance duk wani sabani na siyasa a ƙoƙarin maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar."
"Da yardar Allah za mu magance duk wani saɓani na cikin gida da bambance-bambancen siyasa da ma ƙabilanci da ke cikin rikicin da kuma tabbatar da samun mafita mai ɗorewa."

Shettima Ya Jero Ayyukan da Tinubu Zai Yi a Tudun Biri

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya ce gwamnatin tarayya za ta sake gina garin Tudun Biri bayan harin bam ya yi mummunan barna a makon jiya.

Mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne bayan ya ziyarci ƙauyen da lamarin ya auku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng