Yanzun nan: Lauyoyin Arewa Fiye da 600 Za Su Maka Gwamnatin Tinubu a Kotu, Sun Fadi Dalili

Yanzun nan: Lauyoyin Arewa Fiye da 600 Za Su Maka Gwamnatin Tinubu a Kotu, Sun Fadi Dalili

  • Gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu za ta sake fafatawa a kotu da lauyoyin arewa 600 karkashin inuwar 'Concerned Northern Forum'
  • Lauyoyin sun sha alwashin bi wa yan uwan wadanda abun ya ritsa da su hakkinsu da tabbatar da ganin gwamnati ta biya diyya
  • Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta jajirce wajen daukar matakin da ya dace domin ganin an gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Kungiyar arewa da ta hada lauyoyi sama da 600 ta nuna shirinta na daukar matakin doka a kan gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban kasa Bola Tinubu kan bam da aka jefa kauyen Tudun Biri a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Ribadu da sanatocin arewa sun ziyarci Tudun Biri, sun nuna kwarin gwiwa kan hukumomin tsaro

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, lauyoyin za su dauki matakin ne don tabbatar da ganin cewa gwamnatin Tinubu ta biya diyya ga yan uwan wadanda sojoji suka jefa wa bam a jihar ta arewa maso Yamma.

Sojoji sun ziyarci Tudun Biri
Yanzun nan: Lauyoyin Arewa Fiye da 600 Za Su Maka Gwamnatin Tinubu a Kotu, Sun Fadi Dalili
Asali: Twitter

A ranar Lahadi, 2 ga watan Disamba ne, mutum fiye da 120 suka mutu a wani harin bam da sojoji suka kai wa farin hula bisa kuskure.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barista Nafi’u Abubakar, lauyan da ya yi magana a madadin lauyoyi sama da 600, ya yi bayanin cewa kungiyar za ta yi aiki don tabbatar da ganin cewa yan uwan wadanda abun ya ritsa da su sun samu adalci.

Nafi'u ya fadi hakan ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a Kaduna a ranar Asabar, 9 ga watan Disamba, sannan ya yi kira ga gwamnatin Tinubu da ta jajirce wajen daukar matakin da ya dace domin ganin an gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa kan lamarin.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Lalong ya magantu kan barin majalisar Tinubu ko komawa majalisar dattawa

Jawabinsa na cewa:

"Ya zama wajibi a hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika, kuma a samar da matakan hana sake afkuwar irin wannan lamari a nan gaba."

Kungiyar ta kuma yi kira ga sojojin Najeriya da su sake duba ka'idojin aiki tare da horar da jami'ai don gujewa hasarar rayukan da ba su ji ba ba su gani ba.

Ta yi gargadin cewa dole ne sojoji su yi taka-tsan-tsan wajen gudanar da ayyukansu kasancewar sun shafi fararen hula.

Kungiyar mai dauke da mambobi sama da 600 ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan da suka rasa yan uwansu a wannan mummunan lamari, New Telegraph ta rahoto.

Wani mamba na kungiyar wanda lauya ne mazaunin Kaduna ya ce:

"Ita wannan kungiya ka san wasu lauyoyi ne na arewa daga jihohi mabanbanta. Abubuwa da ake yi a arewa ya dame su, yadda ake ciwa mutanenmu zarafi, da yadda gwamnati ke yin kisan kiyashi kuma bata yin komai.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya ɗauki wasu muhimman matakai masu kyau kan jefa wa Musulmi bam a Tudun Biri

"Sai wannan abun da ya faru na yankin nan sai ya kara tada kowa ya shiga taitayin shi saboda irin wannan abun an yi a Maiduguri, an yi a Jos, Nasarawa da wurare da dama ba wani abu da aka yi.
"Toh wannan da aka yi sai aka ce dole a dage a ga gwamnati ta yi wani abu, wannan ya sa lauyoyi suka hadu, farko dai muka fara hada kanmu a soshiyal midiya na kungiya daga baya kuma aka sa wasu kwamiti ina ciki, muka je muka bincika wadanda suka mutu, muka gane cewa wajen mutum 120 aka kashe, wajen sama da mutum 60 kuma suna asibitin FUTO da Barau Dikko da kuma wasu dai nan Kawo, don haka muka ce dole fa mu dage tsaye abun da dai muke so mu sa gwamnati, shi wanda ke kula d ragamar jirgin yakin da ya sakar wa mutane bam, a fiddo su cikin sojoji domin a hukunta su, na daya.

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna Sani ya caccaki kalaman DHQ kan dalilin jefa bam a taron Musulmai, ya nemi abu 1

“Na biyu za mu dage mu maka kotu kara a kan sai tabbass diyar wadannan mutane sun fito, kuma diyarsu ba yadda aka saba biyan diyya miliyan biyu, miliyan biyar ko miliyan 10 ba, a’a diyya yadda ake biyan diyya a mudulunci. A cikinsu akwai wanda ba Musulmi ba wajen mutum biyu ko uku ne da yake yankin akwai wanda Musulmi akwai wanda ba Musulmi ba. Toh mu dai za mu dage sai an biya su diyya saboda irin wannan sai an samu wata kungiya da za ta dunga tsawatarwa a yankin arewa.
“Manyanmu sun yi shiru ko a kungiyar lauyoyi, ka ga kungiyar lauyoyi ta kasa sun yi shiru, kungiyar Musulmai ta yi shiru sai da muka matsa ne ma naga kungiyar lauyoyi ta Kaduna ta yi magana har sun fidda jawabin manema labarai. Amma dai ace an saka bam sama da mutum 120 sun mutu, wasu 60 kuma sun jikkata wannan ba abun ayi shiru bane.

Kara karanta wannan

Kano: Yarinyar da Abba Kabir ya dauki nauyin jinyarta ta riga mu gidan gaskiya, bayanai sun fito

"Yanzu dai mun yi taro na manema labarai, abu na gaba da za mu yi shine mu shigar da kara, mu yi karar ita hukumar soji da kuma gwamnatin tarayya don ganin hakkin wadannan mutane ya fita."

El-Rufai ya ziyarci Tudun Biri

A wani labarin, mun kawo a baya cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai da amininsa tsohon Sarkin Kano, Mai daraja Muhammadu Sanusi II, sun ziyarci kauyen Tudun biri da ke jihar Kaduna.

El-Rufai da Sanusi sun isa yankin ne domin jajantawa dangin Musulman da aka kashe a harin bama-baman da sojoji suka yi kuskuren jefawa yan farar hula.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng