Ma'aikata Za Su Dara Yayin da Gwamnan APC Ya Yi Musu Wani Muhimmin Abu 1

Ma'aikata Za Su Dara Yayin da Gwamnan APC Ya Yi Musu Wani Muhimmin Abu 1

  • Gwamnan jihar Kebbi ya amince da biyan kuɗin giratuti ga ma'aikata 745 da suka yi ritaya ko suka rasu a jihar
  • Gwamnan ya amince da fitar da N1,795,505,173.08 ga ma'aikatan na jiha, ƙananna hukumomi, ma'aikatar ilmi ta ƙananan hukumomi da ma'aikatan kwangila
  • Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da shugaban ma'aikatan jihar ya fitar inda ya ce an amince da fitar da kuɗin ne bayan an tantance ma'aikatan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya amince da fitar da Naira 1,795,505,173.08 domin biyan kuɗin giratuti ga ma'aikatan da suka yi ritaya da waɗanda suka rasu a jihar.

Biyan kuɗaɗen zai shafi ma'aikata 745 na jiha, ƙananan hukumomi, ma'aikatar ilmi ta ƙananan hukumomi da ma'aikatan kwangila daga ranar 15 ga watan Mayu zuwa 15 ga watan Oktoban 2023, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Rayukan mutum 16 sun salwanta, wasu mutum 27 sun jikkata a wani mummunan hatsarin mota

Gwamna Nasir ya amince da biyan kudin gratuti
Ma'aikata za su samu kudin gratuti a Kebbi Hoto: Nasir Idris
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikata na jihar Kebbi, Alhaji Sufyanu Garba Bena ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi ranar Juma’a, 8 ga watan Disamban 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma'aikata nawa ne za su amfana?

Sanarwar ta ce, ma’aikata 745 da suka yi ritaya, ofishin shugaban ma’aikata ne ya yi binciki tare da tantance su ta hanyar kwamitin da ya ƙunshi ƙungiyoyin ƙwadago da sauran masu ruwa da tsaki.

A cewar sanarwar, kuɗin giratuti na ma'aikata 318 da suka yi ritaya ko suka rasu da ma'aikatan kwangila ya kai N972,710,4.

Kuɗin gratuti da na ma'aikata 247 na ƙananan hukumomi sun kai N427,971,191,33 yayin da kuɗin giratuti na ma'aikata 180 na ma'aikatar ilmi ta ƙananan hukumomi sun kai N394,823,495.83, wanda hakan ya sanya jimillar kuɗin suka kai N1.795,505,173,08.

Kara karanta wannan

Atiku da Ɗangote sun lale Naira biliyan uku sun baiwa ɗan takarar gwamna a arewa? Gaskiya ta yi halinta

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin jihar Kebbi mai suna Lukman Isah wanda ya yaba da wannan ƙuɗirin da gwamnan ya yi na biyan ma'aikatan haƙƙoƙinsu.

Ya bayyana cewa biyan kuɗin ba ƙaramin taimakawa ma'aikatan zai yi ba tare da iyalan waɗanda suka rasu duba da yanayin halin matsin tattalin arziƙin da ake ciki.

"Lallai wannan abun a yaba ne kuma gwamna ya yi ƙoƙari muna fatan Allah ya saka masa sa alkhairi." A cewarsa.

Obaseki Ya Amince da Biyan Albashin Watan 13

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya amince da biyan ma'aikatan jihar albashin watan 13.

Gwamnatin dai za ta biya albashin watan Disamba a ranar Litinin 11 ga watan Disamba, yayin da ma’aikata za su samu albashin watan 13 a ranar Laraba 27 ga watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng