Ribadu da Sanatocin Arewa Sun Ziyarci Tudun Biri, Sun Nuna Kwarin Gwiwa Kan Hukumomin Tsaro
- Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu ya ziyarci kauyen Tudun Biri don yin jaje ga al'ummar yankin
- Haka kuma, sanatocin arewa ma sun kai ziyara yankin da sojoji suka sakarwa masu Maulidi bama-bamai bisa kuskure wanda ya yi sanadiyar rasa rayuwa da dama
- Duk da wannan hari, Ribadu da sanatocin arewar sun nuna kwarin gwiwa kan ayyukan hukumomin tsaro a yankin arewacin kasar
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Mai ba kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu da sanatocin arewa sun nuna kwarin gwiwa kan hukumomin tsaron kasar duk da sakin bama-bamai da sojoji suka yi bisa kuskure a kauyen Tudun Biri da ke kamaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna.
Yayin da aka tabbatar da mutuwar mutum 85 a harin tare da jikkatan wasu da dama a harin, Ribadu da yan majalisar sun yaba jajircewar hukumomin tsaro wajen magance matsalolin tsaro a yankin, Channels TV ta rahoto.
Mai ba kasa shawara kan tsaron ya yi jinjinar ne lokacin da ya ziyarci kauyen Tudun Biri domin binciken kwakwaf, ya kuma bayar da tabbacin cewa ba za a rufe batun harin bam din ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, Ribadu ya yi alkawarin cewa nan ba da jimawa ba za a fara bincike don dakile sake faruwar irin haka a gaba, rahoton Peoples Gazette.
Ya ce:
"Mun zo nan ne domin gani da ido da kuma tattaunawa kai tsaye da mutanen, wadanda abun ya ritsa da su da danginsu da kuma tattarawa gwamnatin tarayya bayanai. Abun bakin ciki da takaici ne. Amma ya faru. Abun da ya rage shine yadda za a ci gaba da rayuwa, darasin da za mu koya daga nan, da kuma abun da ya kamata mu yi."
Ribadu ya yaba ma Uba Sani
Ya kuma yaba ma Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna kan yadda ya nuna dattako da shugabanci mai kyau wajen kula da abun takaicin, musamman wajen samawa wadanda abun ya ritsa da kayan rage radadi da sauransu.
Sanataocin arewa karkashin jagorancin Sanata Abdul Ningo ma sun ziyarci Gwamna Sani don yi masa ta'aziyya kan harin bam din.
Sanatocin arewa sun yi kira ga yan Najeriya
Yayin da suke nuna alhininsu kan lamarin, Sanatocin sun yaba ma hukumomin tsaro kan nasarar da suka samu a yaki da ta'addanci da yan bindiga a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.
Sun kuma roki yan Najeriya a kan su ajiye son zuciya kan lamarin sannan su bar gwamnati ta yi bincike da kai a kan al'amarin domin gujema sake afkuwar irin haka a gaba.
Yayin da yake bayyana kwarin guiwar cewa wadanda harin ya rutsa da su za su samu adalci, Gwamna Sani ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta sake duba wasu tsofaffin dokoki da za su karfafa hukumomin tsaro wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulkin kasar ya dora musu.
El-Rufai da Sanusi sun ziyarci Tudun Biri
A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai da amininsa tsohon Sarkin Kano, Mai daraja Muhammadu Sanusi II, sun ziyarci kauyen Tudun biri da ke jihar Kaduna.
El-Rufai da Sanusi sun isa yankin ne domin jajantawa dangin Musulman da aka kashe a harin bama-baman da sojoji suka yi kuskuren jefawa yan farar hula.
Asali: Legit.ng